Koma ka ga abin da ke ciki

HALITTARSA AKA YI?

Tsuntsayen gannet suna shiga ruwa

Tsuntsayen gannet suna shiga ruwa

 Gannet tsuntsaye ne masu girma sosai kuma suna shiga teku da gudun kilomita 190 cikin awa guda. Idan tsuntsun yana so ya shiga teku, karfin da yake yin haka yana wuce karfin maganadiso sau 20. Me ya sa wadannan tsuntsayen ba sa jin rauni sa’ad da suka shiga teku da irin wannan gudun?

 Alal misali: Kafin tsuntsun ya shiga ruwa da karfin gaske, yana mai da fikafikansa baya, ya sa jikinsa ya zama kamar kwari, yana kuma kāre idanunsa. Yana hura wuyarsa da kuma kirjinsa ya zama kamar balan-balan domin kada ya ji rauni idan ya shiga ruwa n.

 Sa’ad da tsuntsun yake shiga ruwan, yana mike bakinsa da wuyarsa da kuma kansa su zama kamar bututu. Yin hakan yana sa dukan jijiyoyin wuyar tsuntsun su kāre shi. Nan da nan sai ya sake saita idanunsa domin ya iya gani a cikin ruwa.

 Zurfin kafa nawa ne tsuntsun yake iya kai a cikin teku? Idan tsuntsun ya shiga ruwan da karfi sosai, yana kai kusan zurfin kafa 36. Amma yana iya ci gaba da shiga cikin tekun ta wajen kada fukafukansa da ya dan nade da kuma yin amfani da kafafunsa. A wasu lokuta zurfin da suke kai a cikin teku yana wuce kafa 82. Sa’ad da tsuntsun yake fitowa daga ruwan, yana yin hakan a saukake, kuma yana a shirye ya soma firiya.

 Ka kalli yadda tsuntsayen gannet suke shigan ruwa

 Masanan kimiyya sun bi tsarin wannan tsuntsun don su kera na’urar nemo mutane da kuma ceto su daga cikin ruwa. Sun kera na’urar ta rika firiya da shiga ruwa da kuma sake tashi. Amma a lokacin da ake gwada na’urar, daya cikinsu ya yi kaca-kaca domin ta shiga ruwan da karfi sosai. Hakan ya sa ’yan kimiyya su kammala cewa na’urar da suka kera “ba za ta iya shiga ruwa kamar yadda tsuntsun gannet yake yi ba.”

 Mene ne ra’ayinka? Yadda tsuntsun gannet yake shigan ruwa da gudu sakamakon juyin halitta ne? Ko akwai wanda ya halicce shi?