Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Sifata Ce Ta Fi Mini Muhimmanci?

Sifata Ce Ta Fi Mini Muhimmanci?

 Wasa kwakwalwa: Sifata Ce Ta Fi Mini Muhimmanci?

  1.   Wanne cikin furuci na gaban nan ya kwatanta yadda kike ji?

    •  Ba na taba gamsuwa da adona ba.

    •  A wani lokaci na kan so adona.

    •  A ko yaushe ina son adon da nake yi.

  2.   Me za ka so ka canza a jikinka?

    •  Tsayi

    •  Kiba

    •  Sifar jiki

    •  Suma

    •  Launin fata

    •  Girman jiki

    •  Wasu fannoni

  3.   Ka kammala sauran furuci na gaba.

     Ba na son yadda jikina yake. . .

    •  sa’ad da na hau ma’auni.

    •  sa’ad da na duba madubi.

    •  sa’ad da na gwada kaina da wasu, wato, (abokai, ’yan yayi, ’yan wasa).

  4.   Ka kammala wadannan furucin.

     Na kan auna nauyi na . . .

    •  kowacce rana.

    •  kowane mako.

    •  Fiye da sau daya a mako.

  5.   Wanne cikin furucin ya yi daidai da yadda ka ke ji?

    •  Sifar jiki marar kyau. (Misali: Serena ta ce: “Duk lokacin da na duba madubi, sai na ga wata kibabbiya, mummunar sifa. Har sai na ki cin abinci wai don na rage kibata.”)

    •  Sifar jiki da ta dace. (Misali: Natanya ta ce: “Ko yaushe za mu ga wani abin da ba ma so a jikinmu, wasun su ba za mu iya maganinsa ba. Wawanci ne mu nace a kan abin da ba za mu iya maganinsa ba.”)

 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana kada mu ‘aza kanmu gaba da inda ya kamata.’ (Romawa 12:3) Saboda haka, ya dace kuma daidai ne mu aza kanmu yadda ya kamata. Alal misali, abin da ya sa ke nan kake wanke bakinka kuma kana kula da tsabtar jikinka.

 Idan kuma kin damu kwarai game da sifar jikinki fa, har ma yana ci miki rai? Idan haka ne, zai yi kyau ki yi tunanin wannan . . .

 ‘Me ya sa nake da mummunar sifa?’

 Da akwai dalilai da yawa. Sun kunshi:

  •  Tasirin hanyoyin sadarwa. Kellie ta ce: “Hotunan mutane masu kyaun gani, masu tsini da matasa suke gani a telebijin ko da yaushe yana shafansu. Domin haka, ba ma farin ciki idan ba mu yi irin adonsu ba!”

  •  Tasiri daga iyaye. Rita ta ce: “Na lura cewa idan uwata ta mai da hankali sosai da adonta, hakan ya kan shafi yadda yarinyar za ta ji game da yadda take ado. Wannan haka yake game da ubanni da suke da yara maza.”

  •  Sai ki ji ba ki da mutunci. Jeanne ta ce: “Mutane da suka fi mai da hankali game da sifarsu suna son mutane su yaba musu idan suka yi ado. Wannan zai sa ba za ki so ku yi tafiya tare da ita ba!”

 Ko da mene ne ya faru, za ki iya tunani cewa . . .

 ‘Ya kamata na canza yadda na ke ado?’

 Ki saurari abin da wasu tsararki suka ce.

 Rori ta ce: “Ba za ki iya canza sifarki ba, zai dace ki kyale wasu lahani kawai. Idan ki ka kyale lahanin, yawancin mutane ba za su ma san abin da ke faruwa ba.”

 Olivia ta ce: “Ki yi iyakacin kokarinki ki kula da lafiyar jikinki. Idan ki ka yi haka fa za a ga kyaunki. Wanda ba ya son yadda ki ke, (da yake son ki yi kama da wata) to, ba ya sonki da gaske.”

 Batun shi ne: Ki yi iyakacin kokarinki a adana jikinki. Manta da sauran. Yawan damuwa game da adonki zai iya kasance da hadari (Duba “ Labarin Julia.”)

 Erin ta lura cewa idan ki ka kasance da halin daidaita abubuwa, zai taimake ki ki daure da yadda ki ke. Ta ce: “Hakika na kan razana, amma na lura cewa ina bakin ciki idan na mai da hankali kan abubuwa marasa amfani. Abin da nake yi yanzu shi ne wasan motsa jiki kuma na ci abinci mai gina jiki. Sai a ci kwalliya kawai.”

 Ci kwalliya mafi kyau!

 Za ki fi kyau sosai ma idan kin daidaita yadda ki ke ji game da adon jikinki. Littafi Mai Tsarki zai taimaka. Ya ce mu yi abubuwan nan na gaba:

  •  Gamsuwa. “Gwamma abin da ido ke gani, da a yi sha’awa barkatai: wannan kuma banza ne; cin iska kawai.”—Mai-Wa’azi 6:9.

  •  Ki daidaita a wasan motsa jikinki. “Wasan jiki tana da amfaninta kadan.”​—1 Timotawus 4:8.

  •  Kyaun halin kirki. “Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai, amma Ubangiji yakan dubi zuciya.”​—1 Sama’ila 16:7.

 Sarah ta ce: “Fuskarmu takan nuna abin da ke cikin zuciyarmu. Idan mutumin ba ya alhini, mai fara’a ke nan.”

 Phylicia ta ce: “An fi mai da hankali ga kyaun mutum na zahiri. Amma nagarin halayen mutumin ne musamman ake tuna da su.”

 Duba Misalai 11:22; Kolosiyawa 3:​10, 12; 1 Bitrus 3:​3, 4.