Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Alamar “Kwanakin Karshe”?

Mene ne Alamar “Kwanakin Karshe”?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Littafi Mai Tsarki ya fadi abubuwa da yanayoyi da halayen mutane da za su nuna cewa muna “kwanakin karshe” da kuma za su taimaka mana mu fahimci cewa zamanin nan ya kusan ‘karewa.’​—2 Timoti 3:1; Matiyu 24:3; Daniyel 8:19; Mai Makamantu Ayoyi.

Wadanne annabce-annabce ne ke Littafi Mai Tsarki game da “kwanakin karshe”?

 Littafi Mai Tsarki ya fadi abubuwa da yawa da za su zama “alama” da za ta nuna cewa muna kwanakin karshe. (Luka 21:7) Ga wasu cikin su:

 Za a yi yaki a duka duniya. Yesu ya ce: “Alꞌumma za ta tasar wa alꞌumma, mulki ya tasar wa mulki.” (Matiyu 24:7) Littafin Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 6:4 ma ya yi annabci cewa akwai wani mai doki da ke wakiltar yaki da zai “kawar da salama daga duniya.”

 Yunwa. Yesu ya ce: “Za a kuma yi yunwa.” (Matiyu 24:7) Littafin Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna ya sake yin annabci game da wani doki kuma da zai sa a yi yunwa a wurare da yawa a duniya.​—Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 6:​5, 6.

 Girgizar kasa. Yesu ya ce za a yi “rawar kasa a wurare dabam-dabam.” (Matiyu 24:7; Luka 21:11) Wannan rawar kasa ko girgizar kasa da ake yi a wurare dabam-dabam a duniya zai sa mutane da yawa su sha wahala ko kuma su mutu.

 Cututtuka. Yesu ya ce za a yi annoba ko cututtuka masu tsanani.​—Luka 21:11.

 Aikata laifi. Ko da yake an yi darurruwan shekaru ana aikata mugunta, Yesu ya annabta cewa a kwanakin karshe “mugunta” za ta karu ba kadan ba.​—Matiyu 24:12.

 Za a lalata duniya. Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 11:18 ta annabta cewa mutane za su rika “halaka duniya.” Za su yi hakan a hanyoyi da yawa. Ta wurin yin abubuwa marasa kyau da kuma lalatar da muhallinmu.

 Halaye marasa kyau. Littafin 2 Timoti 3:​1-4, ya annabta cewa mutane za su zama “marasa godiya, marasa tsarki, . . . masu rike juna a zuciya, masu bata sunayen wadansu, marasa kame kansu, marasa tausayi, masu kin nagarta, masu cin amana, marasa hankali, masu cika da daga kai.” Da yake mutane za su rika nuna halayen nan sosai, za a kwatanta zamaninmu da lokacin da “za a sha wahala sosai.”

 Tabarbarewar iyali. A littafin 2 Timoti 3:​2, 3, Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa mutane da yawa za su zama “marasa kauna” ga ꞌyan iyalinsu. Kuma yara za su zama “marasa biyayya ga iyayensu.”

 Mutane ba za su kaunaci Allah sosai ba. Yesu ya ce: “Kaunar da yawancin mutane suke yi wa juna za ta ragu.” (Matiyu 24:12) Abin da Yesu yake nufi shi ne mutane ba za su kaunaci Allah kamar yadda suka saba ba. Haka ma 2 Timoti 3:4 ya ce a kwanakin karshe, irin wadannan mutanen za su so “jin dadin kansu fiye da son Allah.”

 Munafunci a addini. A littafin 2 Timoti 3:​5, Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa mutane za su yi daꞌawa suna bauta wa Allah amma ba za su yi nufinsa ba.

 Za a fahimci annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki fiye da dā. Littafin Daniyel ya annabta cewa a “kwanakin karshe,” ilimin mutane da yawa za ya karu kuma za su fahimci annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki.​—Daniyel 12:4.

 Za a yi waꞌazi a fadin duniya. Yesu ya ce: “Za a ba da wannan labari mai dadi na mulkin sama domin shaida ga dukan al’umma.”​—Matiyu 24:14.

 Mutane za su rika kiyayya da baꞌa. Yesu ya annabta cewa mutane ba za su mai da hankali ga abubuwan da suke nuna cewa muna kwanakin karshe ba. (Matiyu 24:​37-39) Fiye da haka ma, littafin 2 Bitrus 3:​3, 4 ya annabta cewa wasu mutane za su rika cewa, ba abin da ya canja, ai kome yana tafiya daidai kamar dā.

 Duka annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki za su cika. Yesu ya ce duka annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki za su cika daya bayan daya a kwanakin karshe, ba kawai kadan daga cikinsu ko kuma yawancinsu ba.​—Matiyu 24:33.

Shin muna rayuwa a “kwanakin karshe”?

 E. Abubuwa da suke faruwa a duniya da tarihin Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa kwankin karshe ya soma ne a shekara ta 1914, a shekarar ne aka soma Yakin Duniya na I. Don ka ga yadda abubuwan da suke faruwa a duniya suke nuna cewa muna kwanaki na karshe, ka kalli bidiyon nan:

 A shekara ta 1914 ne, Mulkin Allah ya soma sarauta a sama. Kuma abu na farko da ya soma yi shi ne ya koro Shaidan da aljannunsa daga sama zuwa duniya kuma ba za su iya komawa sama ba, sai dai su rika kai da kawowa a duniya. (Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 12:​7-12) Muna ganin yadda Shaidan yake rinjayar mutane ta wurin zuga su su rika nuna halaye da yin ayyuka marasa kyau. Kuma wadannan abubuwan da suke yi ne ya sa mutane suke ‘shan wahala sosai.’​—2 Timoti 3:1.

 Mutane da yawa suna bakin ciki don wadannan abubuwa da suke faruwa. Sun damu cewa mutane ba sa iya zaman lafiya da juna. Kuma suna ganin wata rana, mutane za su kashe junansu duka.

 Amma wasu ma da suke bakin ciki game da abubuwan da suke faruwa suna begen cewa rayuwa za ta yi kyau a nan gaba. Suna da tabbaci cewa nan ba da dadewa ba, Mulkin Allah zai kawar da dukan matsalolin da muke fama da su a duniya. (Daniyel 2:44; Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 21:​3, 4) Suna hakuri suna jiran lokacin da Allah zai cika alkawuransa. Ban da haka ma, suna samun karfafa a kalaman Yesu cewa: “Wanda ya jimre har zuwa karshe, zai tsira.”​—Matiyu 24:13; Mika 7:7.