Koma ka ga abin da ke ciki

Kimiyya ta Jitu da Littafi Mai Tsarki Kuwa?

Kimiyya ta Jitu da Littafi Mai Tsarki Kuwa?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 E, ko da yake Littafi Mai Tsarki ba littafi ne na kimiyya ba amma sa’ad da yake zance a kan kimiyya daidai yake. Ga wasu misalai da suka nuna cewa kimiyya da Littafi Mai Tsarki sun jitu. Akwai misalai cikin Littafi Mai Tsarki da suke nuna abin da kimiyya ta ce da aka yarda da su da dadewa ko da yake sun bambanta kwarai da abin da mutane suka gaskata da shi a lokacin.

  •   Akwai tushen sararin halitta. (Farawa 1:1) Kage da aka yi dā sun nuna cewa ba a halicci sararin samaniya ba, amma cewa ya fito ne daga wani yamutsi da ya auku. Mutanen Babila sun yarda cewa allolin da aka sami sararin halitta daga wajensu sun fito ne daga tekuna biyu. Wasu kagen sun ce sararin halitta ya fito ne daga wani katon kwai.

  •   Dokokin da aka sanya cikin sararin halitta ne ke sarrafa shi ba wasu gumaka ba. (Ayuba 38:33; Irmiya 33:25) Kage daga duniya kewaye suna koyar da cewa ’yan Adam ba su da mai taimaka musu sa’ad da suka fuskanci wani tsausayi ko kuma mugunta daga wajen alloli.

  •   An rataye duniya ba a kan kome ba. (Ayuba 26:7) Mutanen dā sun yarda da cewa an shimfida duniya ne a kan manyan dabbobi irin su bauna ko kuma kififfiya.

  •   Ruwan da ya daskare a sama ta wurinsa ne ake samun ruwan sama, mai kankara da suke gudu zuwa cikin koguna da rafuffuka. (Ayuba 36:27, 28; Mai-Wa’azi 1:7; Ishaya 55:10; Amos 9:6) Helenawa na dā sun gaskata cewa ruwan kogi daga cikin kasa ne kuma wannan ra’ayin ya kai karni na 18.

  •   Cewa tuddai suna fitowa ne kuma sukan bace har da tuddai da ake ganinsu a yau. (Zabura 104:6, 8) Amma fa wasu kagen sun nuna cewa alloli ne suka halicci tuddai.

  •   Tsabta tana kawo lafiyar jiki. Dokar da aka ba wa al’ummar Isra’ila ta ce mutum ya wanke hannu bayan da ya taba gawa, a ware wadanda suke da cuta da zai iya kama wasu kuma ta ce a binne najasa. (Levitikus 11:28; 13:1-5; Kubawar Shari’a 23:13) Amma, a lokacin ne ake amfani da wani maganin da Masarawa suke shafa wa idon gembo wanda ake hada shi da najasar mutane.

Akwai wasu kurakure na kimiyya cikin Littafi Mai Tsarki ne?

 A’a, bisa bincike da aka yi cikin Littafi Mai Tsarki. Ga wasu kurakure da ake yi na cewa kimiyyar Littafi Mai Tsarki ba daidai ba ne:

 Kage: Wai Littafi Mai Tsarki ya ce an halicci sararin halitta a kwanaki shida na tsawon sa’o’i 24 ne.

 Gaskiya: Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce shi ne, babu ainihin kwanan wata ko shekara da Allah ya halicci sararin halitta da shi. (Farawa 1:1) Ranakun halitta da aka nuna a Farawa sura 1, kwanaki ne da ba a ambata tsawonsu ba. Hakika, an kira tsawon lokacin da aka yi amfani da shi a halittar sama da duniya “rana.”—Farawa 2:4.

 Kage: Wai Littafi Mai Tsarki ya ce an halicci ciyayi kafin rana don tsire tsire su iya samun amfanin rana.—Farawa 1:11, 16.

 Gaskiya: Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa an halicci rana, wato daya cikin taurari da suke “sammai” kafin a halicci tsire-tsire. (Farawa 1:1) A cikin “rana” na farko na halitta ne haske ya kai duniya. Da yake an sami isashen haske da ya kai ko’ina, wannan ya isa tsire-tsire su sami amfanin rana. (Farawa 1:3-5, 12, 13) Amma ya dan dade kafin aka iya ganin rana daga duniya.—Farawa 1:16.

 Kage: Wai Littafi Mai Tsarki ya ce rana ce ke kewaya duniya.

 Gaskiya: Mai-Wa’azi 1:5 ya ce: “Rana kuwa ta kan fito, ta kan fādi, ta kan yi hanzarin zuwa wurin da ta fito.” Hakika, wannan yana nuna abin da ke faruwa ne daga duniya idan aka kalli rana a sama. Har yau, ana iya cewa “fitowa” da kuma “fadiwar” rana ko da yake an sani cewa duniya ce take kewayar rana.

 Kage: Wai Littafi Mai Tsarki ya ce duniya shimfida ce mai kusurwa hudu.

 Gaskiya: Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da wannan furuci “iyakan duniya,” amma ba ya nufin cewa duniya shimfida ce da take da kusurwa ba. (Ayyukan Manzanni 1:8) Haka ma yake da wannan furucin, “kusurwoyi hudu na duniya” wanda yake nufin duniya kewaye; alal misali, za a iya amfani da gabas, yamma, arewa da kuma kudu don kwatanta wani waje.—Ishaya 11:12; Luka 13:29.

 Kage: Wai Littafi Mai Tsarki ya ce kewayar da’ira fadin layinta uku ne cak, wannan ba daidai ba ne, yana da ’yan kai.

 Gaskiyar: Gwaji da aka yi wa “tabki zubabbe” da aka ambata a 1 Sarakuna 7:23 da kuma 2 Labarbaru 4:2 ya ce “tsayinsa kamu biyar ne, kewayensa kuma kamu talatin.” Watakila lambobin nan ne suka yi kusa da kirgen da aka yi. Mai yiwuwa ne kuma cewa kewayar ciki da kuma fadi na waje ba daidai ba ne.