Koma ka ga abin da ke ciki

Rayuwa Tana da Ma’ana Kuwa?

Rayuwa Tana da Ma’ana Kuwa?

Amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da

 Tambayoyi game da ma’anar rayuwa suna zuwa a fasaloli dabam-dabam kamar su, Me ya sa aka halicce mu? ko kuma Rayuwata tana da ma’ana kuwa? Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa dalilin da ya sa aka halicce mu shi ne mu kulla dangantaka da Allah. Ka lura da wasu abubuwan da ke Littafi Mai Tsarki da suka tabbatar da hakan.

  •   Allah ne Mahaliccinmu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “[Allah] ne ya yi mu” ba mu muka halicci kanmu ba.—Zabura 100:3; Ru’ya ta Yohanna 4:11.

  •   Allah yana da dalilin da ya sa ya halicci kowane abu, har da mu ma.—Ishaya 45:18.

  •   Allah ya halicce mu da “bukatar kulla dangantaka da” shi. (Matta 5:3, fassarar New World Translation) Yana so mu biya wa kanmu wannan bukatar.—Zabura 145:16.

  •   Za mu iya biya wa kanmu wannan bukatar ta wajen kulla abokantaka da Allah. Wasu suna iya ganin kamar ba zai taba yiwuwa mu zama abokan Allah ba, amma Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gare ku.”—Yakub 4:8; 2:23.

  •   Kafin mu zama abokan Allah, wajibi ne mu yi rayuwar da ta jitu da nufinsa. Littafi Mai Tsarki ya bayyana wannan nufin a Mai-Wa’azi 12:13 cewa: “Ka ji tsoron Allah, ka kiyaye dokokinsa; gama wannan kadai ne wajibin mutum.”

  •   A nan gaba, za mu ga ainihi yadda Allah ya so rayuwarmu ta kasance. A lokacin, Allah zai kawar da wahala kuma ya ba da rai madawwami ga abokansa, wato wadanda suka bauta masa.—Zabura 37:10, 11.