Koma ka ga abin da ke ciki

12 GA DISAMBA, 2019
South Korea

Labarin Shaidun Jehobah a Koriya

Labarin Shaidun Jehobah a Koriya

Mutane kalilan ne suka san cewa an tsananta wa Shaidun Jehobah a kasar Koriya a dā. Wani Ma’adanar Ajiye Kayan Tarihi da ake kira National Memorial Museum of Forced Mobilization under Japanese Occupation da ke Busan, birni na biyu mafi girma a Koriya ta nuna yadda aka tsananta wa Shaidun. An fara wannan nuni na musamman da ke da jigo “Changing History, Unchanging Conscience” a ranar 12 ga Nuwamba 2019. Kuma za a kammala a ranar 13 ga Disamba 2019. An ba da labarin yadda Shaidun Jehobah suka ki saka hannu a batun siyasa fiye da shekaru 80 da suka shige a Koriya a lokacin mulkin mallakar Jafanis kuma an bayyana yadda hukumomi suka tsananta musu.

An yi irin wannan nuni a lokaci na farko a watan Satumba 2019 a Ma’adanar Kayan Tarihin * da ke birnin Seoul a Koriya. Baki 51,175 ne suka ziyarci wurin har da ’yan’uwa 5,700 da suka halarci taron kasashe da aka yi a Seoul.

Wannan abin da ya faru a Deungdaesa ya faru ne a lokacin da aka kama Shaidun Jehobah da wasu da suke son sakon Littafi Mai Tsarki kuma aka saka su a kurkuku daga Yuni 1939 zuwa Agusta 1945. An kai wadannan mutane gidan yarin ne don sun ki yi wa sarki sujada kuma suna rarraba kasidu da ake ganin yana hana mutane saka hannu a yaki. Mutane sittin da shida ne aka kama, kusan dukan Shaidun Jehobah da ke zama a Koriya ke nan a wannan lokacin. Wadanda aka tsare a kurkukun sun fuskanci matsi da azaba. Shaidu guda shida sun yi rashin lafiya kuma suka mutu saboda yanayin kurkukun.

Dan’uwa Hong Dae-il wanda ke aiki a Sashen Ba da Rahoto a ofishinmu da ke Koriya ya ce: “Mutane da yawa a Koriya ba su san cewa batun kin shiga aikin soja ya soma ne tun 80 da suka shige a lokacin mulkin mallakar Jafanis ba. Wannan nuni na musamman shi ne na farko da ya ba da damar ba da wannan kyakkyawar labari mai ban mamaki.”

Wani farfesan tarihi mai suna Han Hong-gu da ya halarci bikin tunawa da wadanda aka tsananta wa don bangaskiyarsu, ya ce game da Shaidun Jehobah: “Na amince cewa sun kafa misali mai kyau don yadda suka rike imaninsu. . . . Da zarar al’ummai sun yarda su girmama wadanda suka ki yin yaki domin lamirinsu, wadannan ne ya kamata a fara tunawa da su.”

Masanan tarihi da kuma ’yan jaridu sun nuna cewa suna son wannan nuni da aka yi. Hakan ya ba da damar ilimantar da al’umma a kan tarihin wadanda suka ki shiga aikin soja don imaninsu kuma wannan batu ne da mutane da yawa suke son samun karin haske a kai a Koriya a shekaru da suka shige. A ranar 28 ga Yuni 2018, kotu ta yanke hukunci cewa rashin kirkiro aikin farin hula ga wadanda suka ki yin aikin soja ya saba wa dokar kasar. Bayan wata hudu, a ranar 1 ga Nuwamba, Kotun Koli ta yanke hukunci cewa wadanda suka ki yin aikin soja don imaninsu ba su taka doka ba. Wannan hukunci da Kotun Koli ta yanke ya sa an saki ’yan’uwanmu da ke kurkuku da aka tsare don sun ki shiga aikin soja don imaninsu a Koriya ta Kudu kuma hakan ya sa an tsara dokoki kasar yadda za a iya samar da aikin farin hula.

Irin bangaskiya da karfin zuciya da ’yan’uwanmu a Koriya a dā suka nuna da aka gabatar a nunin ya tuna mana da abin da wani marubucin zabura ya fada. Ya ce. “Yahweh yana tare da ni, ba zan ji tsoro ba, me mutum zai iya yi mini?”​—⁠Zabura 118:⁠6.

^ sakin layi na 3 Kafin a mayar da majami’ar History Hall wurin adana kayan tarihi, ana amfani da shi a matsayin kurkuku don na yi wa mutanen da suka ki shiga aikin soja horo daga shekara ta 1960 zuwa 1989 da kuma Shaidun Jehobah a lokacin mulkin Jafan.

 

Majami’ar Seodaemun Prison History Hall da ke Seoul, Koriya. An yi nuni na farko a watan Satumba 2019 a wurin

Dalibai sun taru a wajen Deungdaesa Incident exhibition a ma’adanar kayan tarihi na History Hall. Kuma mutane wajen of 51,175 suna ziyartar wurin

A nunin da aka yi a wurin, an nuna irin Hasumiyar Tsaro da aka yi amfani da su a kurkukun

Wani dakin da ke nuna irin mawuyacin hali da Shaidun Jehobah suka fuskanta a kurkukun

Ma’adanar ajiye kayan tarihi na Busan National Memorial Museum of Forced Mobilization under Japanese Occupation ce take yin nunin

An kammala nunin da hotunan da suka ba da labarin abin da mutanen 66 fuskanta domin sun ki saka hannu a siyasa