Albishiri Daga Allah!

Wane albishiri ne daga Allah? Me ya sa za mu gaskata da shi? A wannan ƙasidar, an tattauna tambayoyin Littafi Mai Tsarki da aka saba yi.

Yadda Za Ka Amfana Daga Wannan Ƙasidar

Wannan ƙasidar za ta sa ka ji daɗin koyo daga Littafi Mai Tsarki. Ka ga yadda za ka iya yin amfani da Littafi Mai Tsarki naka don ka iya buɗe wasu ayoyin Nassi.

LESSON 1

Mene Ne Albishirin?

Ka koyi game da wannan albishirin da abin da ya sa ya yi gaggawa da kuma abin da ya kamata mu yi.

LESSON 2

Wane Ne Allah na Gaskiya?

Shin Allah yana da suna ne kuma yana kula da mu kuwa?

LESSON 3

Albishirin da ke Cikin Littafi Mai Tsarki Ainihi Daga Allah Ne?

Ta yaya za mu tabbata cewa abin da ke ciki Littafi Mai Tsarki gaskiya ne?

LESSON 4

Wane Ne Yesu Kristi?

Ka koya abin da ya sa Yesu ya mutu, ma’anar fansa, da kuma abin da Yesu yake yi a yanzu.

LESSON 5

Mene Ne Nufin Allah ga Duniya?

Littafi Mai Tsarki ya bayyana dalilin da ya sa Allah ya halicci duniya, lokacin da za a daina shan wahala, da kuma abin da zai faru da wannan duniyar da kuma waɗanda suke cikinta.

LESSON 6

Wane Bege Ne Matattu Suke da Shi?

Mene ne yanayin matattu? Shin za mu sake ganin ƙaunatattunmu da suka mutu kuwa?

LESSON 7

Mene Ne Mulkin Allah?

Wane ne Sarkin Mulkin Allah, kuma mene ne Mulkin zai cim ma?

LESSON 8

Me Ya Sa Allah Ya Ƙyale Mugunta da Wahala?

Ta yaya aka soma mugunta, kuma me ya sa Allah ya ƙyale ta ci gaba? Shin za a daina shan wahala kuwa?

LESSON 9

Me Zai Sa Iyalinka Ta Yi Farin Ciki?

Jehobah, Allah mai farin ciki, yana so iyalai su yi farin ciki. Ka duba shawarar da Littafi Mai Tsarki ya ba wa miji da mata da iyaye da kuma yara.

LESSON 10

Ta Yaya Ne Za Ka Gane Bauta ta Gaskiya?

Shin addini na gaskiya guda ɗaya ne tak? Ka bincika abubuwa 5 da suka nuna masu bauta ta gaskiya.

LESSON 11

Ta Yaya Ne Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki Suke Amfanar Mu?

Yesu ya bayyana dalilin da ya sa muke bukatar ja-gora, da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki biyu da suka fi muhimmanci.

LESSON 12

Ta Yaya Za Ka Iya Zama Aminin Allah?

Ka san ko Allah yana amsa dukan addu’a, yadda ya kamata mu yi addu’a, da kuma wasu abubuwan da za mu yi don mu iya zama aminan Allah.

LESSON 13

Wane Albishiri ne Ake da Shi Game da Addini?

Shin akwai lokacin da kowa za su taru waje ɗaya don bauta wa Allah makaɗaici na gaskiya?

LESSON 14

Me Ya Sa Allah Yake da Ƙungiya?

Littafi Mai Tsarki ya bayyana dalilin da ya sa da kuma yadda Kiristoci na gaskiya suke da haɗin kai.

LESSON 15

Me Ya Sa Ya Kamata Ka Ci Gaba?

Ta yaya sanin Allah da kuma Kalmarsa da ka yi zai amfane wasu? Wace dangantaka ce za ka more da Allah?