Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA GOMA SHA UKU

Ya Koyi Darasi Daga Kuskurensa

Ya Koyi Darasi Daga Kuskurensa

1, 2. (a) Mene ne sakamakon kuskuren da Yunana ya yi? (b) Ta yaya labarin Yunana zai iya taimaka mana?

YUNANA ya so da a ce yana da iko ya sa ko’ina ya yi tsit. Ba iska mai ƙarfi da ke girgiza jirgin ko kuma manya-manyan raƙuman ruwa da suke tura jirgin hagu da dama ne kawai suke damun Yunana ba. Amma, ihun da ma’aikatan jirgin suke yi sa’ad da suke ƙoƙari su hana jirgin nitsewa ne ya fi damunsa. Yunana ya san cewa waɗannan mutanen suna dab da halaka saboda shi!

2 Me ya sa Yunana ya shiga irin wannan mugun yanayin? Ya yi babban kuskure wajen hulɗarsa da Jehobah. Wane irin kuskure ne ya yi? Shin dangantakarsa da Allah ta yi tsami ne gabaki ɗaya? Amsoshin waɗannan tambayoyin za su koya mana darussa da yawa. Alal misali, labarin Yunana ya taimaka mana mu fahimci cewa waɗanda suke da bangaskiya ma suna iya yin kuskure, kuma su yi gyara.

Annabi Bagalile

3-5. (a) Mene ne mutane suka fi mai da wa hankali sa’ad da aka ambata Yunana? (b) Wane bayani ne aka ba da game da tarihin Yunana? (Ka kuma duba hasiya.) (c) Me ya sa hidimar Yunana ba mai sauƙi ko kuma mai daɗi ba ce?

3 Duk sa’ad da aka ambata Yunana, mutane sukan fi mai da hankali ga kuskurensa, kamar rashin biyayya ko kuma taurin kai. Amma, akwai abubuwa da yawa da ya kamata mu sani game da wannan mutumin. Ya kamata mu tuna cewa Jehobah ne ya zaɓe shi ya zama annabi. Da a ce ba shi da aminci ko kuma adalci, da Jehobah bai zaɓe shi ya yi wannan gagarumin aikin ba.

4 Littafi Mai Tsarki ya ɗan faɗi tarihin Yunana. (Karanta 2 Sarakuna 14:25.) Yunana ɗan Gath-hepher ne, garin da ke da nisan mil biyu da rabi daga Nazarat. Yesu Kristi ya yi girma a wannan garin kusan shekara 800 bayan zamanin Yunana. * Yunana annabi ne a lokacin sarautar Sarki Jeroboam na biyu na ƙabila goma na Isra’ila. Zamanin Iliya ya wuce, kuma magajinsa Elisha ya mutu a lokacin sarautar mahaifin Jeroboam. Ko da yake Jehobah ya yi amfani da waɗannan mutanen don kawar da bautar Baal, amma Isra’ilawa sun fara komawa gidan jiya. Mutanen suna bin misalin sarki wanda ya ci gaba da yin “mugunta a gaban Ubangiji.” (2 Sar. 14:24) Shi ya sa hidimar Yunana ba za ta kasance da sauƙi ba. Duk da haka, ya yi hidimarsa da aminci.

5 Wata rana, sai salon rayuwar Yunana ya canja gabaki ɗaya. Jehobah ya ba shi aikin da ya yi masa wuya ƙwarai da gaske. Wane irin aiki ke nan?

‘Tashi, Ka Tafi Nineba’

6. Wane aiki ne Jehobah ya ba Yunana, kuma me ya sa aikin kamar yana da wuya ainun?

6 Jehobah ya gaya wa Yunana: ‘Tashi, ka tafi Nineba, babban birnin nan, ka tada murya, ka faɗace ta, gama muguntarsu ta hau gaba gareni.’ (Yun. 1:2) Yanzu mun fahimci abin da ya sa wannan aikin ya kasance mai wuya ainun. Nineba tana da nisan mil 500 kuma tana a gabas, ƙila tafiyar wajen wata ɗaya ne da kafa. Amma, ba wahalar tafiyar ba ce ta fi damun Yunana. Assuriyawan birnin Nineba mutane ne masu mugunta da nuna ƙarfi, kuma Yunana zai sanar musu da saƙon hukunci da Jehobah zai yi musu. Tun da Yunana bai ga canji sosai daga mutanen Allah ba, me zai gani daga wajen arna? Ta yaya Yunana kaɗai zai yi nasara a Nineba babban birnin nan, wanda kuma za a soma kiransa “birni mai-jini”?—Nah. 3:1, 7.

7, 8. (a) Ta yaya Yunana ya ƙudura niyya ya ƙi yin aikin da Jehobah ya ba shi? (b) Me ya sa za mu ce Yunana ba matsoraci ba ne?

7 Shin Yunana ya yi wa kansa waɗannan tambayoyin kuwa? Ba mu san da hakan ba, amma abin da muka sani shi ne cewa ya gudu. Jehobah ya aike Yunana zuwa gabas, amma ya nufi yamma. Ya je gaɓar teku da ke garin da ake kira Yafa, idan ya sami jirgin da zai je birnin Tarshish. Wasu masana sun ce birnin Tarshish yana ƙasar Sifen. Idan haka ne, Yunana ya yi tafiya zuwa inda ke da nisan mil 2,200 daga Nineba. Irin wannan tafiya a cikin jirgin ruwa zuwa ƙarshen Babbar Teku, zai iya ɗaukan dogon lokaci har tsawon shekara ɗaya! Yunana ya ƙudura niyya ya ƙi yin aikin da Jehobah ya ba shi!—Karanta Yunana 1:3.

8 Shin hakan yana nufin cewa Yunana matsoraci ne? Ko kaɗan. A sakin layi na gaba, za mu tattauna wasu abubuwa da suka nuna cewa Yunana yana da gaba gaɗi. Yunana ajizi ne kamar kowannenmu, kuma yana fama da kasawarsa. (Zab. 51:5) Wane ne a cikinmu bai taɓa jin tsoro ba?

9. Yaya za mu iya ji game da aikin da Jehobah ya ba mu, kuma mene ne muke bukatar mu tuna idan hakan ya faru?

9 A wasu lokatai, muna iya ji kamar wani abu da Allah ya ce mu yi yana da wuya ko kuma ya fi ƙarfinmu. Muna iya jin tsoron yin wa’azin Mulkin Allah da aka ce mu yi. (Mat. 24:14) Tun da yake mu ajizai ne, ba shi da wuya mu mance da abin da Yesu ya ce: “Ga Allah abubuwa duka ya yiwu.” (Mar. 10:27) Za mu fahimci matsalar da Yunana ya fuskanta, sa’ad da muka tuna cewa mu ajizai ne. Mene ne sakamakon gudun da Yunana ya yi?

Jehobah Ya Yi wa Annabinsa Marar Biyayya Horo

10, 11. (a) Mene ne Yunana yake tunani sa’ad da jirgin ya soma tafiya? (b) Wane hadari ne ya faɗa wa jirgin da matuƙansa?

10 Ka yi tunanin yadda Yunana yake zaune cikin jirgin ruwa, yana kallo sa’ad da matuƙin jirgin da ma’aikatansa suna ƙoƙari su soma tafiya da jirgin. Sa’ad da suka soma tafiya, wataƙila Yunana ya yi tsammanin ya guje wa abin da ke sa shi tsoro. Amma, nan da nan sai ƙiɗa ta canja.

11 Iska mai ƙarfi da kuma raƙuman ruwa masu girma da za su iya nitsar da jiragen ruwa na zamani sun mamaye tekun. Iska da raƙuman ruwa sun yi ta gaba da baya da jirgin. Shin a lokacin da ake wannan guguwar, Yunana ya san cewa Jehobah ne ya “aike da babban iska cikin teku”? Ba mu sani ba. Amma dai ya ga matuƙan jirgin suna roƙon allolinsu, kuma ya san cewa allolin ƙarya ba za su taimaka musu ba. (Lev. 19:4) Yunana ya ce: “Jirgin yana bakin fashewa.” (Yun. 1:4) Yaya Yunana zai yi addu’a ga Allahn da ya ƙi zuwa aikansa?

12. (a) Me ya sa ba za mu yi saurin shar’anta Yunana don yana barci sa’ad da ake hadari? (Ka kuma duba hasiya.) (b) Ta yaya Jehobah ya fallasa sanadiyyar guguwar?

12 Sa’ad da Yunana ya kasa taimaka musu, sai ya nemi waje a can cikin jirgin ya kwanta. A nan ne ya share barci. * Matuƙin jirgin ya ga Yunana yana barci, sai ya tashe shi, ya ce ya yi addu’a ga Allahnsa kamar yadda kowa yake yi. Ma’aikatan jirgin sun tabbata cewa da akwai dalilin wannan hadarin, sai suka jefa ƙuri’a don su ga ko wane ne sanadiyyar wannan matsalar. Babu shakka, gaban Yunana ya faɗi sa’ad da ƙuri’a take cire mutane ɗai-ɗai. Nan da nan sai gaskiya ta fito. Jehobah ne yake ja-gorar hadari da kuma ƙuri’ar da ta faɗa a kan Yunana.—Karanta Yunana 1:5-7.

13. (a) Mene ne Yunana ya gaya wa matuƙan jirgin? (b) Mene ne ya ce matuƙan jirgin su yi, kuma me ya sa?

13 Yunana ya gaya wa ma’aikatan jirgin duk abin da ya faru. Shi bawan Allah Maɗaukaki ne, Jehobah. Shi ne Allahn da yake guje wa kuma shi ne ya sa su cikin wannan haɗarin. Abin da Yunana ya gaya wa mutanen ya ba su mamaki ƙwarai, kuma ya ga cewa sun tsorata. Suka tambaye shi abin da za su yi don kada su da jirgin su halaka. Mene ne Yunana ya ce? Wataƙila ya yi tunanin yadda zai nitse a cikin wannan teku mai zurfi. Amma, me ya sa Yunana zai ƙyale waɗannan mutanen su halaka bayan zai iya cetonsu? Sai ya ce musu: “Ku ɗauke ni, ku jefa ni cikin teku; da hakanan teku za ya yi muku sauƙi ya kwanta; gama na sani saboda ni ne wannan babban hadari ya same ku.”—Yun. 1:12.

14, 15. (a) Ta yaya za mu yi koyi da bangaskiyar Yunana? (b) Mene ne matuƙan jirgin suka yi sa’ad da Yunana ya ce su jefa shi cikin teku?

14 Matsoraci ba zai iya furta irin waɗannan kalaman ba. Hakika, sadaukar da kai da Yunana ya yi a wannan lokaci mai wuya, ta faranta wa Jehobah rai. A nan mun ga cewa Yunana yana da bangaskiya sosai. Za mu iya yin koyi da wannan ta wurin saka bukatun wasu gaba da namu. (Yoh. 13:34, 35) Idan muka ga wani yana bukatar taimako ko yana baƙin ciki ko kuma yana bukatar ƙarfafa don ya ci gaba da bauta wa Jehobah, ya kamata mu taimaka masa. Jehobah zai yi farin ciki idan muka yi hakan!

15 Wataƙila abin da Yunana ya gaya wa matuƙan jirgin ya dame su, shi ya sa da farko suka ƙi yin abin da ya ce su yi. Sun yi iya ƙoƙarinsu don su wuce hadarin, amma sun kasa. Hadari sai ƙara tsanani yake yi. Daga baya, sai suka ga cewa ba su da na yi. Sai suka roƙi Jehobah Allahn Yunana ya yi musu jin ƙai, suka ɗauke shi suka jefa shi cikin teku.—Yun. 1:13-15.

Ma’aikatan jirgin sun jefa Yunana cikin teku kamar yadda ya umurce su

An Yi wa Yunana Jin Ƙai Kuma An Cece Shi

16, 17. Ka kwatanta abin da ya faru da Yunana sa’ad da aka jefa shi cikin teku. (Ka kuma duba hotunan.)

16 Yunana ya faɗa cikin ruwa. Wataƙila ya yi ƙoƙari ya yi iyo don kada ya nitse cikin ruwan, kuma don ya tabbata cewa jirgin yana tafiya da kyau. Amma sai raƙumin ruwa ya tura shi ƙasan tekun. Ya nitse ƙasa, yana tunanin ya gama yawo.

17 Daga baya, Yunana ya kwatanta yadda ya ji a wannan lokaci. Yana ta tunanin abubuwa dabam-dabam. Yana baƙin ciki cewa ba zai sake ganin haikali mai kyau na Jehobah da ke Urushalima ba. Ya ga yadda yake nitsewa har ƙasan tekun, kusa da tussan duwatsu inda abubuwa da suka tsira a cikin teku suka kakkama shi. Yana ganin kamar wurin ne zai zama kabarinsa.—Karanta Yunana 2:2-6.

18, 19. Mene ne ya faru da Yunana a cikin teku, wane irin kifi ne ya haɗiye shi, kuma wane ne ya sa waɗannan abubuwa suka faru? (Ka kuma duba hasiya.)

18 Amma, akwai wani abu mai rai da ke matsowa kusa, baƙi ne kuma babba. Yana zuwa kusa da Yunana da sauri. Sai ya buɗe bakinsa ya haɗiye Yunana.

Jehobah ya ‘shirya babban kifi ya haɗiye Yunana’

19 Wataƙila Yunana yana ganin cewa nan zai mutu. Duk da haka, ya ga abin mamaki. Ya ga cewa dabbar ba ta cinye shi ba, kuma yana nan da rai, ko da yake yana wurin da ya kamata ya zama kabarinsa. Yunana ya yi ta mamaki. Babu shakka, Allahnsa Jehobah ne ya “shirya baban kifi” don ya haɗiye shi. *Yun. 1:17.

20. Mene ne za mu iya koya game da Yunana daga addu’ar da ya yi a cikin babban kifi?

20 Lokaci yana shigewa, har ya kai awoyi. A nan cikin irin duhun da Yunana bai taɓa gani ba, ya yi addu’a ga Jehobah Allah. Addu’ar da ya yi tana rubuce a sura ta biyu na littafin Yunana. Hakan ya nuna cewa Yunana ya san Nassosi sosai, saboda sau da yawa ya ambata Zabura. Ya kuma nuna yana da halin yin hamdala. Yunana ya kammala: “Amma ni, da muryar godiya zan yi maka hadaya; zan biya abin da na yi wa’adinsa. Ceto na Ubangiji ne.”—Yun. 2:9.

21. Mene ne Yunana ya koya game da ceto, kuma wane darasi mai muhimmanci ne ya kamata mu koya?

21 Yunana ya koya cewa Jehobah zai iya ceton kowa, a duk inda yake kuma a kowane lokaci. Har a “cikin cikin kifi,” Jehobah ya ceci bawansa da ke cikin matsala. (Yun. 1:17) Jehobah ne kaɗai zai iya sa mutum ya rayu kwana uku a cikin babban kifi. Ya kamata mu tuna cewa Jehobah shi ne ‘Allah wanda numfashinmu yana hannunsa.’ (Dan. 5:23) Numfashinmu da ranmu suna hannunsa. Shin muna yin godiya kuwa don hakan? Tun da Jehobah ne ya halicce mu, ya kamata mu riƙa yi masa biyayya.

22, 23. (a) Ta yaya Jehobah ya gwada Yunana don ya ga ko ya tuba da gaske? (b) Mene ne za mu iya koya daga Yunana idan muka yi kuskure?

22 Shin Yunana ya koyi yin biyayya ga Jehobah kuwa? E. Bayan kwana uku, kifin ya zo gaɓar teku ya yi aman Yunana, kuma “ya zubar da shi a gaci.” (Yun. 2:10) Jehobah ya taimaki Yunana ta wurin sa kifin ya kai shi gaɓar teku! Amma daga gaɓar tekun, ya soma neman duk inda hanya take. Ba da daɗewa ba, Jehobah ya gwada Yunana ko ya tuba da gaske. Yunana 3:1, 2 sun ce: ‘Sai maganar Ubangiji ta zo wurin Yunana, zuwa na biyu, cewa, Tashi, ka tafi Nineba, babban birnin nan, ka faɗace ta da faɗaka wadda na umurce ka.’ Mene ne Yunana zai yi?

23 Yunana bai yi jinkiri ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Yunana fa ya tashi, ya tafi Nineba bisa ga maganar Ubangiji.’ (Yun. 3:3) Ya yi biyayya. Hakika, ya koyi darasi daga kuskurensa kuma. Muna bukatar mu yi koyi da bangaskiyar Yunana domin dukanmu muna yin kuskure. (Rom. 3:23) Amma, shin muna yin sanyin gwiwa ko kuma muna koyan darasi daga kuskurenmu kuma mu yi biyayya ga Allah kuwa?

24, 25. (a) Wace albarka ce Yunana ya samu? (b) Wace albarka ce zai samu a nan gaba?

24 Jehobah ya albarkaci Yunana don biyayyarsa kuwa? Ƙwarai kuwa. Na farko, wataƙila Yunana ya sami labari cewa waɗanda suke cikin jirgin sun tsira. Hadarin ya lafa nan da nan bayan da suka jefa Yunana cikin teku, kuma waɗanda suke cikin jirgin suka “ji tsoron Ubangiji ƙwarai” suka yi hadaya ga Jehobah maimakon allolinsu na ƙarya.—Yun. 1:15, 16.

25 Daga baya, ya sami wata albarka mafi girma. Yesu ya yi amfani da lokacin da Yunana yake cikin kifi don kwatanta yadda zai kasance a kabari. (Karanta Matta 12:38-40.) Sa’ad da aka ta da Yunana daga matattu, zai yi farin ciki jin hakan! (Yoh. 5:28, 29) Kai ma, Jehobah yana son ya albarkace ka. Ka riƙa koyon darasi daga kuskurenka kamar yadda Yunana ya yi, ka yi biyayya kuma ka kasance da halin sadaukar da kai!

^ sakin layi na 4 Yana da muhimmanci cewa Yunana asalin ɗan Galili ne domin Farisawa sun ce game da Yesu: “Ka bi ciki, ka gani, daga cikin Galili babu annabin da ke fitowa.” (Yoh. 7:52) Mafassara da yawa da masu bincike sun ce wai Farisawa suna nufi cewa, ba a taɓa samun annabi Bagalile ba kuma ba za a taɓa samu ba. Idan haka ne, waɗannan mutanen sun yi watsi da tarihi da kuma annabci.—Isha. 9:1, 2.

^ sakin layi na 12 Don nanata irin barcin da Yunana ya yi, wata fassara ta ce ya yi barci har da minshari. Amma, maimakon mu yi tunanin cewa Yunana bai kula da abin da ke faruwa da jirgin ba, za mu iya tuna cewa a wani lokaci, barci yakan kwashi waɗanda suke da damuwa. A lokacin da Yesu yake cikin azaba a lambun Jathsaimani, Bulus da Yaƙub da Yohanna sun yi “barci domin baƙinciki.”—Luk 22:45.

^ sakin layi na 19 Idan aka fassara kalmar nan “kifi” a Ibrananci zuwa Helenanci, yana nufin “dodon teku” ko kuma “babban kifi.” Ko da yake babu yadda za a san ko wace irin halitta ce wannan, amma an lura cewa akwai manya-manyan kifaye a Bahar Maliya da za su iya haɗiye mutum ɗungum. Akwai manya-manyan kifaye a wasu wurare, wani babban kifin yana iya kai tsawon kafa 45 ko kuma fiye da haka!

Duk da kuskuren da Yunana ya yi, yana da halaye masu kyau