Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Tattaunawa tun da wuri yana da muhimmanci

Idan Wani Naka Yana Rashin Lafiya Mai Tsanani

Idan Wani Naka Yana Rashin Lafiya Mai Tsanani

WESLEY yana da shekara 54 sa’ad da likita ya ce yana da kansar ƙwaƙwalwa kuma hakan ya girgiza matarsa Doreen sosai. * Likitoci sun ce nan da watanni kaɗan zai mutu. Doreen ta ce, “Abin da suka gaya min ya girgiza ni sosai. Na yi makonni da yawa ba na iya yin kome. Ji nake kamar mafarki nake yi. Ban san cewa hakan zai faru ba.”

Hakika, da akwai mutane da yawa da suke ji kamar Doreen. Mutum yana iya kamuwa da cuta mai tsanani a kowane lokaci. Kuma akwai mutane da yawa da suke ba da kansu don su kula da mai rashin lafiya. Ya kamata a gode musu. Duk da haka, kula da marar lafiya yana da wuya. Mene ne iyalai za su yi don su kula da wani nasu da yake rashin lafiya mai tsanani? Yaya waɗanda suke kula da marar lafiya za su iya bi da yanayin? Mene ne ya kamata su yi yayin da marar lafiya yake gab da mutuwa? Da farko, bari mu yi la’akari da dalilin da ya sa kula da marar lafiya yake da wuya a zamaninmu.

ƘALUBALEN DA AKE FUSKANTA A YAU

Ci gaban da aka samu a fannin kiwon lafiya ya sa mutane ba sa mutuwa kamar dā. A shekarun da suka shige, mutane suna mutuwa sosai a sakamakon cututtuka ko kuma hatsari har ma a ƙasashen da aka samu ci gaba. Babu asibitoci sosai a lokacin. Don haka, iyalan yawancin mutane da suke rashin lafiya ne suke kula da su har su mutu a gida.

Amma a yanzu, an sami ci gaba a fannin kiwon lafiya da har likitoci suna maganin wasu munanan cututtuka. Cututtukan da za su iya kashe mutum nan da nan a dā ana iya maganin su yanzu. Amma, wasu magungunan ba sa iya warƙar da mutum. Yawancin mutane suna samun cututtukan da suke hana su kula da kansu. Kuma kula da irin waɗannan marasa lafiya ba shi da sauƙi sam.

A yau, mutane da yawa suna mutuwa a asibiti. Kuma da akwai mutane da yawa da ba su san abin da ke faruwa kafin mutum ya mutu ba. Wasu kuma ba su taɓa ganin mutum yana mutuwa ba. Tsoron abin da zai iya faruwa yana iya sa wani da ke kula da marar lafiya sanyin gwiwa. Amma mene ne zai iya taimaka?

KU YI SHIRI TUN DA WURI

Kamar Doreen, mutane da yawa suna baƙin ciki sosai sa’ad da wani nasu yake fama da ciwo mai tsanani. Duk da damuwa da tsoro da kuma baƙin ciki, mene ne zai iya taimaka maka ka yi shiri don abin da zai iya faruwa? Wani bawan Allah ya yi addu’a cewa: “Ka koya mana hikima mu ƙididdiga kwanakinmu, don mu yi rayuwarmu da lura.” (Zabura 90:12) Don haka, ka yi addu’a Jehobah ya nuna maka yadda za ka ‘ƙididdiga kwanakinka’ da kyau don ka kula da wani naka da ba shi da lafiya.

Yin hakan na bukatar shiri sosai. Idan marar lafiyar yana iya magana, zai dace ka tambaye shi wanda yake so ya riƙa yanke masa shawara sa’ad da rashin lafiyarsa ta soma muni. Zai dace ka tattauna da shi ko zai so a farfaɗo da shi, ko a kwantar da shi a asibiti ko kuma a kan irin jinyar da yake so. Yin hakan zai rage samun saɓani a tsakaninku kuma ba zai sa wanda ya yanke masa shawara baƙin ciki ba. Yin shiri tun da wuri da kuma tattaunawa da kyau yana taimaka wa iyalai su mai da hankali a kan kulawa da marar lafiyar. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wurin da babu shawara, nufe-nufe sukan warware.”​—Misalai 15:22.

YADDA ZA KA IYA TAIMAKA

Ainihin abin da mai kula da marar lafiya ya kamata ya yi shi ne ƙarfafa marar lafiyan. Mutumin da yake bakin mutuwa yana bukatar ƙauna da kuma kulawa. Ta yaya za a yi hakan? Ka karanta masa littafi ko kuma ka yi masa waƙar da yake so sosai. Marasa lafiya da yawa suna jin daɗi sa’ad da wani nasu ya riƙe hannunsu kuma yake musu magana a hankali.

Zai dace ka gaya wa marar lafiyan sunayen baƙin da suka zo wurinsa. Wani rahoto ya ce: “Sa’ad da mutum ya soma mutuwa, wasu gaɓoɓin jikinsa sukan daina aiki, amma gaɓa ta ƙarshe da ke daina aiki ita ce kunne. Ko da kana ganin [marar lafiyan] yana barci, zai iya jin abin da kuke faɗa. Don haka, kada ka faɗi abin da ba za ka iya faɗa a gabansa ba.”

Idan zai yiwu, ku yi addu’a tare. Littafi Mai Tsarki ya ambaci wani lokacin da ake tsananta wa manzo Bulus da abokansa sosai da har suke ganin kamar za a kashe su. Mene ne suka yi? Bulus ya gaya wa ’yan’uwansa: “Ku ma sai ku taimake mu da addu’a.” (2 Korintiyawa 1:​8-11, Littafi Mai Tsarki) Yin addu’a tana taimakawa sosai sa’ad da kuke fama da rashin lafiya mai tsanani.

KU GAYA WA KANKU GASKIYA

Ganin cewa wani naka yana bakin mutuwa zai sa ka baƙin ciki sosai. Domin babu wanda yake so ya mutu. Ba a halicce mu don mu riƙa mutuwa ba. (Romawa 5:12) Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce mutuwa ‘maƙiyiyar’ mu ce. (1 Korintiyawa 15:26) Don haka, ba laifi ba ne idan ba ma so wani namu ya mutu.

Amma idan iyalai suna gaya wa kansu gaskiya batun abin da zai iya faruwa, hakan zai rage tsoro kuma zai sa su fi mai da hankali ga kula da marar lafiyan a yadda ya dace. An ambata wasu abubuwan da za su iya faruwa da marar lafiya sa’ad da yake gab da mutuwa a akwatin nan “ Abubuwan da Za Su Iya Faruwa Kafin Mutuwa.” Ko da yake, ba lallai ba ne hakan ya faru ga kowane marar lafiya ko kuma ɗaya bayan ɗaya yadda aka ambata a wannan akwatin. Amma waɗannan abubuwan suna faruwa ga yawancin marasa lafiya.

Idan marar lafiya ya rasu, zai dace ka kira wani abokinka da ya amince zai taimaka. Masu kula da kuma iyalan marar lafiyan suna bukatar a ta’azantar da su kuma a tabbatar musu da cewa wani nasu da ke wahala ya huta. Mahaliccinmu ya gaya mana cewa “matattu ba su san kome ba.”​—Mai-Wa’azi 9:5.

MAI BA DA CIKAKKIYAR KULAWA

Kada mu ƙi taimakon mutane

Kuna bukatar ku dogara ga Jehobah a lokacin da kuke kula da marar lafiyan da kuma bayan mutuwarsa. Jehobah zai taimaka muku ta wurin kalmomi da kuma ayyukan da mutane za su yi muku. Doreen ta ce: “Na koyi kada na ƙi amincewa da taimakon mutane. Domin taimakon da suka yi mana ne ya taimaka mana sosai. Ni da maigidana mun san cewa wannan taimakon kamar Jehobah ne yake gaya mana cewa, ‘Ina tare da ku don in taimaka muku a cikin wannan yanayin.’ Ba zan taɓa mantawa da su ba.”

Hakika, Jehobah Allah ne mai ba da cikakkiyar kulawa. A matsayinsa na mahaliccinmu, ya san damuwarmu da kuma baƙin cikinmu. Yana a shirye ya ba mu taimako da kuma ƙarfafar da muke bukata. Ban da haka ma, ya yi alkawarin cewa zai cire mutuwa gabaki ɗaya kuma zai ta da biliyoyin mutane daga matattu. (Yohanna 5:​28, 29; Ru’ya ta Yohanna 21:​3, 4) A lokacin, dukanmu za mu faɗi kalaman manzo Bulus da ya ce: “Ke mutuwa, ina nasararki? Ke mutuwa, ina dafinki?”​—1 Korintiyawa 15:​55, Juyi Mai Fitar da Ma’ana.

^ sakin layi na 2 An canja suna.