Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Allah Mai Tausayi Ne Kuwa?

Allah Mai Tausayi Ne Kuwa?

ABIN DA HALITTU SUKA KOYA MANA

Tausaya wa mutum yana nufin “ka sa kanka a cikin yanayinsa ta wurin yin tunanin yadda za ka ji idan kai ne ka shiga irin yanayinsa.” Wani masanin Lafiyar Ƙwaƙwalwa mai suna Dakta Rick Hanson ya ce “tausayi yana cikin jininmu.”

KA YI LA’AKARI DA WANNAN: Me ya sa ’yan Adam suke da tausayi fiye da duk sauran halittu masu rai? Littafi Mai Tsarki ya ce domin Allah ya halicce mu a cikin kamaninsa. (Farawa 1:26) Hakan yana nufin cewa mu ’yan Adam muna da halaye masu kyau irin na Allah. Saboda haka, idan muka ga wani ya taimaka wa mabukata saboda tausayi, yana yin koyi ne da Mahaliccinmu Jehobah wanda shi mai tausayi ne.​—Karin Magana 14:31.

LITTAFI MAI TSARKI YA BAYYANA YADDA ALLAH YAKE TAUSAYA MANA

Allah yana tausaya mana kuma ba ya jin daɗi idan muna shan wahala. Ga abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa a kan wahalar da al’ummar Isra’ila ta dā suka sha a ƙasar Masar da kuma shekaru 40 da suka yi a cikin jeji: “A cikin dukan damuwarsu shi ma ya damu.” (Ishaya 63:9) Ayar ba ta ce Allah ya san damuwarsu kawai ba, amma ta nuna cewa ya damu da wahalar da suka sha. Allah ya ce, “Hakika, na san dukan wahalarsu.” (Fitowa 3:7) Ya kuma ƙara cewa, “Duk wanda ya taɓa mutanena ya taɓa ƙwayar idona ne.” (Zakariya 2:8) Saboda haka, yana damunsa idan mutane suka ci mutuncinmu.

Littafi Mai Tsarki ya ba mu tabbaci cewa ko da muna ganin ba mu da daraja kuma ba mu cancanci Allah ya ji tausayinmu ba, “Allah ya fi zuciyarmu ya kuma san dukan kome.” (1 Yohanna 3:​19, 20) Allah ya san mu fiye da yadda muka san kanmu. Ya san irin yanayin da muke ciki da tunaninmu da kuma yadda muke ji. Yana tausaya mana.

Tun da mun san cewa Allah yana taimaka ma waɗanda suke cikin damuwa, za mu iya roƙon sa ya ƙarfafa mu, ya ba mu basira kuma ya taimaka mana

Nassosi sun tabbatar mana cewa

  • “Za ku yi kira, ni Yahweh zan amsa, za ku yi kukan neman taimako, zan kuwa ce, ‘Ga ni nan.’”​—ISHAYA 58:9.

  • ‘Na san irin shirin da nake da shi domin ku. Shiri ne na alheri, ba na masifa ba, domin in ba ku bege da rayuwa ta nan gaba. Ni Yahweh na faɗa. Sa’an nan za ku yi kira gare ni, ku juyo, ku yi addu’a gare ni, ni zan kuwa ji ku.’​—IRMIYA 29:​11, 12.

  • “Ka auna yawan hawayena. Ba a rubuce suke a cikin littafinka ba?”​—ZABURA 56:8.

ALLAH YANA FAHIMTAR YANAYINMU KUMA YANA TAUSAYA MANA

Shin sanin cewa Allah yana tausaya mana zai taimaka mana mu jimre matsaloli? Ka yi la’akari da labarin Maria:

“Bayan ɗana mai shekara 18 ya rasu sanadiyyar ciwon kansa da ya yi shekara biyu yana fama da shi, sai na yi tunanin cewa rayuwa tana cike da wahaloli da rashin adalci. Na yi fushi da Jehobah domin bai taimaka ma yarona ya warke ba!

“Shekaru shida bayan hakan, sai wata abokiyata a ikilisiyarmu da take ƙaunata da tausaya min ta saurare ni da kyau yayin da nake gaya mata dalilin da ya sa na ce Jehobah ba ya ƙaunata. Bayan ta saurare ni na awo’i, sai ta nuna min 1 Yohanna 3:​19, 20, nassin ya ce: ‘Allah ya fi zuciyarmu ya kuma san dukan kome.’ Ta bayyana mini cewa Allah ya san damuwarmu. Wannan nassin ya ƙarfafa ni sosai.

“Duk da haka, ban daina fushin da nake yi ba! Sai na karanta littafin Zabura 94:​19, wurin ya ce: ‘Sa’ad da damuwoyi sukan yi mini yawa, ta’aziyyarka takan ƙarfafa raina.’ Na ji kamar domin ni aka rubuta ayar! A ƙarshe, na ga muhimmanci gaya wa Jehobah damuwata domin na san zai saurare ni kuma ya fahimci damuwata.”

Abin ƙarfafa ne mu san cewa Allah ya san damuwarmu kuma yana tausaya mana! Amma me ya sa wahaloli suka yi yawa? Shin Allah yana mana horo don zunubanmu ne? Allah zai yi wani abu don a daina shan wahala? Za a ba da amsoshin tambayoyin nan a talifi na gaba.