Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ZA KA IYA KUSANTAR ALLAH

Kana Ganin Ka Kusaci Allah Kuwa?

Kana Ganin Ka Kusaci Allah Kuwa?

“Dangantaka ta kud-da-kud da Allah tana ba mutum kwanciyar hankali kuma tana sa ya sami tabbaci cewa bai rasa kome ba. Za ka ji kamar Allah yana kiyaye ka a kowane lokaci.” —IN JI CHRISTOPHER, WANI MATASHI A GANA.

“Allah yana ganin dukan wahalar da kake sha, yana ƙaunarka kuma yana kula da kai fiye da yadda kake tsammani.”—IN JI HANNAH, WATA ’YAR SHEKARA 13 DAGA JIHAR ALASKA, AMIRKA.

“Babu abin da ke sa mutum farin ciki da kwanciyar rai kamar sanin cewa yana da dangantaka ta kud-da-kud da Allah!”—IN JI GINA, WATA ’YAR JAMAIKA MAI SHEKARU WAJEN 45.

Mutane da yawa a faɗin duniya suna da irin ra’ayin Christopher da Hannah da kuma Gina domin sun amince cewa Allah yana ɗaukansu a matsayin aminansa. Kai kuma fa? Kana ganin ka kusaci Allah kuwa? Ko kuwa za ka so ka kusace shi ko ka daɗa kusantarsa? Wataƙila kana tunani cewa, ‘Zai yiwu ɗan Adam ya ƙulla dangantaka ta kud-da-kud da Allah, Maɗaukakin Sarki? Idan hakan zai yiwu, to ta yaya?’

ZAI YIWU KA KUSACI ALLAH

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa zai yiwu mu ƙulla dangantaka ta kud-da-kud da Allah. A cikin Littafi Mai Tsarki, Allah ya kira Ibrahim “aminina.” (Ishaya 41:8) Ka kuma lura da gayyatar da ke littafin Yaƙub 4:8. Ayar ta ce: “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gare ku.” Hakan ya nuna cewa zai yiwu mu ƙulla dangantaka mai kyau da Allah. Amma tun da ba za mu iya ganin Allah ba, ta yaya za mu kusace shi kuma mu ƙulla dangantaka mai kyau da shi?

Kafin mu amsa wannan tambayar, bari mu yi la’akari da yadda abokantaka take somawa tsakanin ’yan Adam. Abokantaka tana somawa ne bayan mutane biyu sun san sunayen juna. Yayin da suke magana da juna a kai a kai kuma suna gaya wa juna ra’ayinsu da yadda suke ji, dangantakarsu za ta daɗa yin danƙo. Kuma idan suna yi wa juna alheri, za su daɗa kusantar juna. Hakan ma yake da ƙulla dangantaka da Allah. Bari mu tattauna abin da ya sa muka faɗi hakan.