Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ƘARSHEN DUNIYA YA KUSA KUWA?

Mutane da Yawa Za Su Tsira—Kai Ma Za Ka Iya Tsira

Mutane da Yawa Za Su Tsira—Kai Ma Za Ka Iya Tsira

Littafi Mai Tsarki ya ce za a yi halaka sa’ad da ƙarshen ya zo: “Za a yi ƙunci mai-girma, irin da ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har yanzu . . . Kuma da ba domin an gajertar da waɗannan kwanaki ba, da ba mai-rai da za ya tsira.” (Matta 24:21, 22) Amma Allah ya yi alkawari cewa mutane da yawa za su tsira: “Duniya ma tana wucewa . . . , amma wanda ya aika nufin Allah ya zauna har abada.”—1 Yohanna 2:17.

Me ya kamata ka yi don ka tsira sa’ad da aka halaka wannan duniya kuma ka rayu “har abada”? Ya kamata ka soma tattara kayayyaki ko kuma yin wasu shirye-shirye don wannan ranar ne? A’a. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa mu kafa wasu maƙasudai dabam. Ya ce: “Tun da yake duk abubuwan nan za a halaka su haka, waɗanne irin mutane ya kamata ku zama? Ya kamata ku yi zaman tsarkaka masu ibada, kuna sauraron ranar Allah, kuna gaggauta zuwanta!” (2 Bitrus 3:10-12, Littafi Mai Tsarki) Mahallin wannan ayar ta nuna cewa “duk waɗannan” abubuwan da za su shuɗe sun ƙunshi masu sarautar wannan muguwar duniyar da dukan waɗanda suke goyon bayan sarautarsu maimakon na Allah. Hakika, idan muka tattara kayayyakin duniya, ba za su cece mu a wannan ranar ba.

Babu shakka, idan muna so mu tsira, ya kamata mu duƙufa yin ibada ga Jehobah kuma mu koyi halaye da ayyuka masu kyau da za su faranta masa rai. (Zafaniya 2:3) Yawancin mutane ba su gaskata cewa ƙarshen ya kusa ba, amma bai kamata mu kasance da irin ra’ayinsu ba. Maimakon haka, zai dace mu riƙa ‘sauraron ranar Allah, muna gaggauta zuwanta.’ Shaidun Jehobah za su nuna maka abin da Littafi Mai Tsarki ya ce ya kamata ka yi don ka tsira a wannan ranar.