Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

KA YI KOYI DA BANGASKIYARSU | SARATU

“Ke Kyakkyawar Mace Ce”

“Ke Kyakkyawar Mace Ce”

SARATU ta tsaya a tsakiyar ɗaki tana kallon ko’ina. Ka yi tunanin irin kyan da wannan ‘yar Gabas ta Tsakiya mai kyawawan idanu take da shi. Shin da akwai alamar damuwa a fuskarta? Idan haka ne, za mu iya sanin dalilin da ya sa take cikin damuwa. Abubuwa da yawa sun faru a wannan gidan. Ita da maigidanta Ibrahim, sun yi shekaru da yawa a gidan. * Kuma hakan ya sa suna son gidan sosai.

Suna zama a Ur, wani babban birni da ke da ƙwararrun maƙera da kuma ‘yan kasuwa. Don haka, suna da dukiya sosai. Amma a wurin Saratu, wannan gidan ba kawai inda take ajiya dukiyoyinta ba ne. A wannan gidan, ita da maigidanta sun yi rayuwa tare a cikin kowane irin yanayi. Kuma sau da yawa, suna yin addu’a ga Jehobah Allahnsu. Babu shakka, waɗannan abubuwan sun sa Saratu ta so wajen nan sosai.

Duk da haka, Saratu ta yarda ta ƙaura daga wannan wurin. Za ta bar gidanta kuma ta tafi inda ba ta sani ba duk da cewa shekarunta wajen 60 ne a lokacin. Ƙari ga haka, rayuwa ba za ta kasance mata da sauƙi a wurin ba kuma babu alama cewa za su sake dawowa. Amma mene ne ya sa za ta yi hakan? Kuma mene ne za mu iya koya daga bangaskiyarta?

“KA FITA DAGA CIKIN ƘASARKA”

Saratu ta yi girma a birnin Ur. Ko da yake an riga an halaka birnin a yanzu. Amma a zamanin Saratu, ‘yan kasuwa suna shigar da kayayyaki masu kyau daga ƙasashe dabam-dabam ta Kogin Yufiretis zuwa wannan babban birnin. Mutane da yawa suna bin hanyar birnin, ga ƙwale-ƙwale da yawa sun taru a tashar jirgin, kasuwar kuma na cike da kayayyaki kala-kala. Ka yi tunanin yadda Saratu ta yi rayuwa a wannan babban birnin tun tana yarinya har ta san sunayen mutane da yawa a birnin. Su ma sun san ta sosai domin ita kyakkyawa ce. Kuma tana da iyali a wajen.

Littafi Mai Tsarki yana yawan cewa ita mace ce mai imani sosai, amma ba allahn-wata wanda ake bauta wa a Ur ne ta yi imani da shi ba. An ƙera wani babban gunki a birnin don wannan allahn. Amma Saratu ta yi imani ne da Allah na gaskiya, wato Jehobah. Littafi Mai Tsarki bai bayyana yadda ta soma bauta wa Jehobah ba. A dā, mahaifinta mai bautar gumaka ne. Sai Saratu ta auri Ibrahim kuma ya girme ta da shekara goma. * (Farawa 17:17) Daga baya, an soma kiran Ibrahim “uban masu-bada gaskiya duka.” (Romawa 4:11) Waɗannan ma’auratan suna daraja juna, suna tattaunawa da kyau, kuma suna magance matsaloli tare, hakan ya ƙarfafa aurensu. Mafi muhimmanci shi ne suna ƙaunar Jehobah sosai.

Saratu tana ƙaunar mijinta sosai kuma su biyun suna zama a birnin Ur tare da danginsu. Ba da daɗewa ba, sai suka fuskanci wata matsala. Littafi Mai Tsarki ya ce Saratu “bakarariya ce; ba ta da ɗa.” (Farawa 11:30) A zamanin Saratu, irin wannan yanayin ba ƙaramin abu ba ne. Duk da haka, ta riƙe amincinta ga Allah da kuma mijinta. Sun ɗauki yaron ɗan’uwansu mai suna Lutu, a matsayin ɗansu domin mahaifinsa ya rasu. Sun ci gaba da rayuwa haka, amma daga baya abubuwa suka canja.

Ibrahim ya zo wurin Saratu yana farin ciki. Yana mamakin abin da ya faru da shi. Allahn da suke bauta wa ya yi magana da shi ta wurin mala’ika! Ka yi tunanin Saratu tana kallon maigidanta da kyawawan idanunta kuma tana tambayarsa cewa: “Mene ne ya gaya maka? Don Allah ka gaya mini!” Wataƙila Ibrahim ya zauna tukuna don ya tattara hankalinsa. Daga baya, sai ya gaya mata cewa Jehobah ya ce: “Ka fita daga cikin ƙasarka, daga danginka kuma, ka taho cikin ƙasa wadda zan nuna maka.” (Ayyukan Manzanni 7:2, 3) Bayan sun yi murna sosai, sai suka soma tunani a kan aikin da Jehobah ya ba su. Za su bar ƙasarsu kuma su je su zauna a wani wuri ba tare da samun gidan kansu ba! Mene ne Saratu za ta ce? Babu shakka, Ibrahim ya kalle ta sosai kuma ya yi tunanin ko za ta ba shi goyon baya a irin wannan aikin da ke gabansu.

Wataƙila ba za mu iya fahimtar yanayin da Saratu take ciki ba. Za mu iya cewa, ‘Allah bai taɓa gaya mini ko maigidana mu yi hakan ba!’ Amma gaskiyar ita ce, dukanmu muna fuskantar irin wannan yanayin. Muna rayuwa ne a duniyar da ke ƙarfafa neman kuɗi ruwa a jallo kuma hakan yana sa mu fi mai da hankali ga yadda za mu ji daɗin rayuwa. Amma Littafi Mai Tsarki ya ce muna bukatar mu fi mai da hankali ga abin da zai faranta wa Allah rai maimakon kanmu. (Matta 6:33) Yayin da muke yin la’akari da abin da Saratu ta yi, mu tambayi kanmu, ‘Wane zaɓi ne zan yi a rayuwata?’

SUN “FITO DAGA CIKIN ƘASAR”

Yayin da Saratu take shirya kaya, ta soma tunanin abubuwan da za ta ɗauka da kuma waɗanda za ta bari. Saboda irin rayuwar da za su yi, ba ta bukatar ta ɗauki kaya masu yawa da za su yi wa jaki ko rakumi nauyi. Don haka, za su sayar da yawancin kayansu ko kuma su ba da su kyauta. Ban da haka, ba za ta ƙara samun zarafin yin abubuwan da ake yi a birni ba kamar su zuwa kasuwa don sayan hatsi da nama da ‘ya’yan itace da tufafi da dai sauransu.

Saratu ta bar duk abubuwan da take mora a birnin Ur don bangaskiyarta

Wataƙila barin gidansu gabaki ɗaya ne ya fi yi wa Saratu wuya sosai. Masu bincike sun gano irin gidajen da ke birnin Ur kuma bincikensu ya nuna cewa Saratu ta sadaukar da abubuwan jin daɗin rayuwa sosai. Wasu gidajen suna da ɗakuna fiye da goma sha biyu da kuma ruwan famfo a ciki. Har ƙananan gidaje ma suna da rufi mai kyau da katanga da ƙofa kuma hakan yana kāre su daga ɓarayi da kuma namomin daji da ake yawan gani a lokacin. Shin zama a tanti zai iya kāre su daga irin waɗannan abubuwan?

Iyalinsu kuma fa? Allah ya ce su ‘fita daga cikin ƙasarsu, daga danginsu kuma.’ Hakan bai kasance wa Saratu da sauƙi ba, domin wane ne za ta tafi ta bari? Babu shakka, wannan kyakkyawar matar mai hankali tana da ‘yan’uwa da yawa da take ƙauna sosai kuma wataƙila ba za ta ƙara ganin su kuma ba. Duk da haka, Saratu ta ci gaba da shirya kayanta don tafiyarsu.

Duk da waɗannan ƙalubalen, Saratu ta gama shirya kome da kome. Terah ne babba a cikin iyalin kuma ya kusan shekara ɗari biyu. Don haka, zai bi Ibrahim da kuma Saratu. (Farawa 11:31) Hakika, Saratu tana da babban aiki, wato kula da wannan dattijon. Lutu ma zai bi su yayin da suke bin umurnin Jehobah kuma suka ‘fita daga cikin ƙasar Kaldiyawa.’Ayyukan Manzanni 7:4.

Sun bi ta Yufiretis kuma suka zo ƙasar Haran mai nisan wajen kilomita 960. Da suka kai Haran, sai suka zauna a wajen na ɗan lokaci. Terah ba shi da lafiya sosai don haka, ba zai iya ci gaba da tafiyar ba. Iyalin sun zauna a wajen har Terah ya mutu yana da shekara 205. Kafin su ci gaba da tafiyarsu, Jehobah ya sake yi wa Ibrahim magana kuma ya gaya masa cewa ya bar ƙasar da suke zuwa inda zai nuna masa. A wannan karon, Allah ya yi alkawari cewa: “Daga wurinka zan yi al’umma mai-girma.” (Farawa 12:2-4) Shekarun Ibrahim 75 sa’ad da suka bar Haran, na Saratu kuma 65 amma ba su da ɗa. Ta yaya Ibrahim zai zama al’umma mai girma? Shin zai ƙara aure ne? A lokacin, maza suna auren mata da yawa. Don haka, wataƙila Saratu ta yi tunanin Ibrahim zai ƙara aure.

Sai suka bar ƙasar Haran kuma suka ci gaba da tafiya. Amma ka lura da waɗanda suke tare da su yanzu. Littafi Mai Tsarki ya ce Ibrahim da iyalinsa sun kwashi dukiyoyi da kuma mutanen da “suka samu cikin Haran.” (Farawa 12:5) Su wane ne waɗannan mutanen da suka samu? Wataƙila bayi ne. Babu mamaki, Ibrahim da Saratu sun gaya wa duk mutanen da suka haɗu da su game da imaninsu. Wasu masu fassara na Yahudawa sun ce mutanen da aka ambata a ayar nan mutane ne da suka soma bauta wa Jehobah tare da Ibrahim da Saratu. Idan haka ne, to bangaskiyar Saratu mai ƙarfi ta sa ta yi wa wasu wa’azi game da Allah da gaba gaɗi. Zai dace mu yi koyi da hakan, domin mutane a zamaninmu ba su da bege sam. Shin za ka iya gaya wa wani game da abin da ka koya a Littafi Mai Tsarki?

SUN JE ƘASAR “MASAR”

Bayan sun tsallake Kogin Yufiretis wataƙila a ranar 14 ga watan Nisan 1943 kafin haihuwar Yesu, sai suka bi ta kudu kuma suka zo ƙasar da Jehobah ya yi musu alkawarinsa. (Fitowa 12:40, 41) Ka ɗauka kana ganin Saratu tana kallon nan da can, yayin da take mamakin kyaun ƙasar. Jehobah ya sake bayyana wa Ibrahim a bishiyar Moreh da ke kusa da Shechem kuma ya ce masa: “Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa.” Wannan kalmar “zuriyarka” ta sa Ibrahim tunani sosai! Ya yi tunanin lokacin da Jehobah ya yi annabci a lambun Adnin cewa wata zuriya za ta halaka Shaiɗan wata rana. Kuma Jehobah ya gaya wa Ibrahim cewa al’ummar da za ta fito daga wurinsa za ta kawo wa ‘yan Adam albarka a nan duniya.Farawa 3:15; 12:2, 3, 6, 7.

Duk da haka, iyalin sun fuskanci matsalolin da ruwan dare gama gari ne a duniya. Saboda karancin abinci a ƙasar Kan’ana, Ibrahim ya ƙaura da iyalinsa zuwa kusa da Masar. Amma ya san cewa zai iya fuskantar matsaloli. Sai ya ce wa Saratu: “Na sani ke kyakkyawar mace ce, lokacin da Masarawa suka gan ki za su ce, ‘Wannan matarsa ce,’ za su kashe ni, amma za su bar ki da rai. Ki ce ke ‘yar’uwata ce, domin dalilinki kome sai ya tafi mini daidai a kuma bar ni da raina.” (Farawa 12:10-13, Littafi Mai Tsarki) Me ya sa Ibrahim ya bukaci Saratu ta yi haka?

Ibrahim ba maƙaryaci ba ne kuma shi ba matsoraci kamar yadda wasu suka faɗa ba. Saratu ’yar’uwarsa ce da gaske kuma matakin da Ibrahim ya ɗauka ya dace. Domin shi da Saratu sun san cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne alkawarin da Allah ya yi cewa zai fitar da zuriya ta musamman da kuma al’umma ta wurinsa. Saboda da haka, matakin da Ibrahim ya ɗauka yana da muhimmanci. Ƙari ga haka, ‘yan tarihi sun gano cewa masu iko a Masar suna yawan ƙwace matan mutane kuma su kashe mazansu. Saboda haka, Ibrahim ya nuna azanci kuma Saratu ta yi biyayya da shi.

Abin da ya faru jim kaɗan bayan haka ya nuna cewa Ibrahim yana da hujjar jin tsoro. Wasu hakiman Fir’auna sun lura cewa Saratu tana da kyau sosai. Sai suka gaya wa Fir’auna game da ita, sai ya aika a kawo ta fādarsa! Ka yi tunanin irin baƙin cikin da Ibrahim ya yi da kuma irin tsoron da Saratu ta ji. Amma ba su wulaƙanta ta ba. Maimakon haka, sun kula da ita da kyau. Wataƙila Fir’auna ya yi hakan ne don ya burge Saratu, sa’an nan sai ya yi yarjejeniya da “ɗan’uwanta,” wato Ibrahim kuma ya aure ta.Farawa 12:14-16.

Ka yi tunanin yadda Saratu ta tsaya tana kallon birnin daga wundon ɗakin. Yaya Saratu ta ji yanzu da take gidan da akwai rufi mai kyau da katanga da kuma abinci mai daɗi? Shin ta yi kwaɗayin zama a irin wannan gidan, wanda mai yiwuwa ya fi dukan dukiyar da take da shi a birnin Ur? Ka yi tunanin irin farin cikin da Shaiɗan zai yi in da a ce Saratu ta bar Ibrahim kuma ta auri Fir’auna! Amma Saratu ba ta yi hakan ba domin tana da aminci ga maigidanta da Jehobah kuma ta daraja aurenta. Zai yi kyau dukan ma’aurata a zamaninmu su riƙa nuna irin wannan amincin! Shin za ka iya yin koyi da Saratu ta wajen riƙe aminci ga ‘yan’uwanka da kuma abokanka?

Arziki da wadatar Fir’auna, ba su sa Saratu ta bar Ibrahim ba

Jehobah ya ɗau mataki don ya kāre wannan mace mai aminci. Ya yi hakan ta wurin tura annoba ga Fir’auna da kuma gidansa. Sa’ad da Fir’auna ya sami labari cewa Saratu matar Ibrahim ce, sai ya ƙyale ta ta koma wurin mijinta kuma ya umurci dukansu su bar ƙasar Masar. (Farawa 12:17-20) Babu shaka, Ibrahim ya yi farin ciki sa’ad da ta dawo! Ka tuna, ya gaya mata cewa: “Na sani ke kyakkyawar mace ce.” Amma akwai abin da ya fi lura da shi game da Saratu, wato halayenta masu kyau kuma irin wannan kyau ne Jehobah yake so. (1 Bitrus 3:1-5) Irin waɗannan halaye ne ya kamata dukanmu mu kasance da su. Za mu iya yin koyi da bangaskiyar Saratu ta wurin saka ayyukan ibada farko a rayuwarmu. Ƙari ga haka, mu riƙa gaya wa wasu abubuwan da muke koya daga Kalmar Allah da kuma bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a duk sa’ad da muke fuskantar jarrabawa.

^ sakin layi na 3 A dā, sunayensu Abram ne da Saraya, amma an fi sanin su da sunan da Jehobah ya ba su.Farawa 17:5, 15.

^ sakin layi na 8 Saratu ‘yar’uwar Ibrahim ce. Mahaifinsu ɗaya ne, wato Terah amma mahaifiyarsu ce ba ɗaya ba. (Farawa 20:12) Ko da yake a yau an haramta yin irin wannan auren, amma yana da muhimmanci mu yi la’akari da yadda rayuwa take a lokacin. Mutane ba su daɗe da zama ajizai ba. Don hakan, irin wannan aure ba zai kawo matsala ga ‘ya’yan da za a haifa ba. Amma abubuwa sun canja bayan wajen shekara 400. Shi ya sa Dokar da Allah ya bayar ta hannun Musa ta haramta auren dangi.Levitikus 18:6.