Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 113

Salamar da Muke Morewa

Salamar da Muke Morewa

(Yohanna 14:27)

  1. 1. Ya Maɗaukaki Allah,

    Uban salama.

    Muna miƙa ma yabo

    Don ayyukanka.

    Ɗanka shi ne Sarkinmu,

    Sarkin Salama.

    Zai cire yaƙe-yaƙe

    A duniyar nan.

  2. 2. Ba ma yin zage-zage,

    Ba ma masifa.

    Mun mai da takubbanmu,

    Zuwa garmuna.

    Mu riƙa gafarta wa

    Dukan mutane.

    Mu yi zaman lafiya

    Kamar Sarkinmu.

  3. 3. Allah ne ke sa mu yi

    Zaman lumana.

    Muna bin dokokinsa

    A kullayaumi.

    Mu bar mutane su san

    Mu Shaidunsa ne,

    Har sai Allah ya kawo

    Salama sosai.

(Ka kuma duba Zab. 46:9; Isha. 2:4; Yaƙ. 3:​17, 18.)