Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 128

Ka Jimre Har Karshe

Ka Jimre Har Karshe

(Matta 24:13)

  1. 1. Duk alkawuran Allahnmu

    Suna ƙarfafamu.

    Abubuwan da mun koya

    Dukansu gaskiya ne.

    Ka zama mai bangaskiya,

    Mai son yin nufin Allah

    Da kuma wa’azi kullum

    Domin ka yi nasara.

  2. 2. Kada ka manta da Allah

    Don zai taimake ka,

    Kuma ka riƙa jimrewa,

    Da kowace wahala.

    Ko kana cikin damuwa,

    Kada ka ji tsoro sam.

    Jehobah na tare da kai

    Domin ya taimake ka.

  3. 3. Waɗanda suka jimre ne

    Za su sami ceto.

    Za su rayu har abada

    Domin sun yi biyayya.

    Bari mu jimre har ƙarshe

    Ko muna shan wahala.

    Allah zai albarkace mu

    Da rai na har abada.

(Ka kuma duba Ibran. 6:19; Yaƙ. 1:4; 2 Bit. 3:12; R. Yoh. 2:4.)