Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 138

Tsofaffi Masu Aminci Suna da Daraja

Tsofaffi Masu Aminci Suna da Daraja

(Misalai 16:31)

  1. 1. ʼYan’uwanmu tsofaffi

    Muna ƙaunar ku.

    Mun san cewa kun jimre

    Da jarrabawa.

    Yanzu ba ku da ƙarfi,

    Kuna ciwo ma.

    Don amincinsu Uba,

    Ka sa su rayu.

    (AMSHI)

    Ya Uba, ka tuna

    Da amincinsu.

    Bari su san cewa

    Kana ƙaunar su.

  2. 2. Tsofaffi amintattu

    Masu daraja.

    Jehobah na ƙaunar su

    Don amincinsu.

    Akwai lokacin da su

    Matasa ne fa,

    Kuma sun yi hidima

    Da ƙwazo sosai.

    (AMSHI)

    Ya Uba, ka tuna

    Da amincinsu.

    Bari su san cewa

    Kana ƙaunar su.

(Ka kuma duba Zab. 71:​9, 18; Mis. 20:29; Mat. 25:​21, 23; Luk. 22:28; 1 Tim. 5:1.)