Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 147

Alkawarin Rai Na Har Abada

Alkawarin Rai Na Har Abada

(Zabura 37:29)

  1. 1. Allah ya yi alkawari,

    Duniya za ta yi kyau.

    ‘Amintattu za su more’

    Rai na har abada.

    (AMSHI)

    Zama a Aljanna

    Zai yi daɗi sosai.

    Allahnmu zai cika

    Alkawuransa.

  2. 2. Rayuwa cikin Aljanna,

    Duk za mu sami ’yanci.

    Za mu sami kwanciyar rai

    Yadda Allah ya ce.

    (AMSHI)

    Zama a Aljanna

    Zai yi daɗi sosai.

    Allahnmu zai cika

    Alkawuransa.

  3. 3. Za a yi tashin matattu,

    Baƙin ciki zai ƙare.

    Jehobah zai taimake mu,

    Zai share hawaye.

    (AMSHI)

    Zama a Aljanna

    Zai yi daɗi sosai.

    Allahnmu zai cika

    Alkawuransa.

(Ka kuma duba Isha. 25:8; Luk. 23:43; Yoh. 11:25; R. Yoh. 21:4.)