Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 2

Jehobah Ne Sunanka

Jehobah Ne Sunanka

(Zabura 83:18)

  1. 1. Ya Allahnmu mai rai,

    Kai ka halicci kome.

    Har abadan abadin,

    Jehobah sunanka.

    Muna alfahari

    Da zama mutanenka.

    Muna shelar girmanka

    A kowace ƙasa.

    (AMSHI)

    Jehobah, Jehobah,

    Babu Allah sai kai.

    Babu wani a can sama

    Ko a nan duniya.

    Kai kaɗai ne Maɗaukaki,

    Babu mai ja da kai.

    Jehobah, Jehobah,

    Kai ne kaɗai fa Allahnmu.

  2. 2. Kana sa mu zama

    Duk abin da kake so,

    Domin mu yi nufinka,

    Jehobah Allahnmu.

    Domin alherinka

    Ka kira mu Shaidunka.

    Ka ba mu babban gata

    Mu amsa sunanka.

    (AMSHI)

    Jehobah, Jehobah,

    Babu Allah sai kai.

    Babu wani a can sama

    Ko a nan duniya.

    Kai kaɗai ne Maɗaukaki,

    Babu mai ja da kai.

    Jehobah, Jehobah,

    Kai ne kaɗai fa Allahnmu.

(Ka kuma duba 2 Laba. 6:14; Zab. 72:19; Isha. 42:8.)