Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 31

Ka Bi Allah!

Ka Bi Allah!

(Mikah 6:8)

  1. 1. Ka bi Allah da sauƙin kai,

    Ka riƙa son gaskiya.

    Ka riƙe aminci ga Allahnmu

    Domin ya ƙarfafa ka.

    Ka dogara da Kalmar Allah

    Don kar a ruɗe ka.

    Ka bar Allah ya bi da kai,

    A cikin rayuwarka.

  2. 2. Ka bi Allah cikin tsarki,

    Ka riƙa yin nagarta.

    Ko da kana fuskantar jarraba,

    Allah zai taimake ka.

    Ka riƙa aikata nagarta

    A duk rayuwarka.

    In ka yi abubuwan nan,

    Allahnmu zai bi da kai.

  3. 3. Ka bi Jehobah da murna

    Domin yana ƙaunar ka.

    Ka gode masa don alherinsa

    Da kuma duk kyautarsa.

    Ka bi Jehobah da daɗin rai,

    Ka yabi sunansa.

    Mutane za su san cewa

    Kai bawan Jehobah ne.

(Ka kuma duba Far. 5:24; 6:9; Filib. 4:8; 1 Tim. 6:​6-8.)