Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 46

Muna Godiya, Ya Jehobah

Muna Godiya, Ya Jehobah

(1 Tasalonikawa 5:18)

  1. 1. Mun gode Jehobah don koyarwarka

    Da muke samu dare da rana.

    Mun gode domin gatan yin addu’a,

    Don mu gaya maka damuwarmu.

  2. 2. Mun gode Jehobah don Ɗanka Yesu,

    Ya ba da ransa don duk mutane.

    Mun gode don kana taimaka mana

    Mu cika dukan alkawuranmu.

  3. 3. Mun gode Allah da ka ba mu gata

    Na yin shelar sunanka mai girma.

    Mun gode don wahala za ta ƙare,

    Albarkar Mulkin za ta dawwama.

(Ka kuma duba Zab. 50:14; 95:2; 147:7; Kol. 3:15.)