Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 59

Mu Yabi Jehobah

Mu Yabi Jehobah

(Zabura 146:2)

  1. 1. Mu yabi Jah,

    Mu yi waƙa!

    Ya nuna mana alheri sosai.

    A koyaushe,

    Mu yabe shi

    Don ƙaunarsa da kuma ikonsa.

    Mu yabe shi, mu yi wa’azi ma.

  2. 2. Mu yabi Jah,

    Yana son mu,

    Yana biyan dukan bukatunmu.

    Yana kula

    Da bayinsa.

    Ruhunsa yana taimaka mana.

    Za mu bauta wa Jehobah kullum.

  3. 3. Mu yabi Jah

    Mai adalci,

    Mu dogara ga Jehobah Allah.

    Zai magance;

    Matsaloli,

    Za mu more albarkar Mulkinsa.

    Ku zo mu ci gaba da yabon sa!

(Ka kuma duba Zab. 94:​18, 19; 145:21; 147:1; 150:2; A. M. 17:25.)