Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 63

Mu Shaidun Jehobah Ne!

Mu Shaidun Jehobah Ne!

(Ishaya 43:​10-12)

  1. 1. Wasu na bautar gunki,

    Ba su san Allahnmu ba.

    Shi ne Maɗaukaki,

    Allahn gaskiya.

    Shi ne ya san duk abin

    Da ke zuwa nan gaba.

    Gumaka ba su san kome ba,

    Shaidunsu maƙaryata ne.

    (AMSHI)

    Mu Shaidun Jehobah ne

    Kuma ba ma jin tsoro.

    Allahnmu shi ne na gaskiya,

    Annabcinsa na cika.

  2. 2. Muna shelar sunansa

    Da kuma ɗaukakarsa.

    Muna yin bishara

    Ta Mulkin Allah.

    Ba ma tsoron wa’azi

    Ga mutanen yankinmu.

    In sun kusaci Maɗaukaki

    Za su yabe shi da ƙwazo.

    (AMSHI)

    Mu Shaidun Jehobah ne

    Kuma ba ma jin tsoro.

    Allahnmu shi ne na gaskiya,

    Annabcinsa na cika.

  3. 3. Yin wa’azi da himma

    Na girmama Allahnmu.

    Gargaɗi ne kuma

    Ga duk mugaye.

    Allah zai yafe masu

    In sun yi tuban gaske.

    Yana wa bayinsa albarka,

    Zai ba su rai har abada.

    (AMSHI)

    Mu Shaidun Jehobah ne

    Kuma ba ma jin tsoro.

    Allahnmu shi ne na gaskiya,

    Annabcinsa na cika.

(Ka kuma duba Isha. 37:19; 55:11; Ezek. 3:19.)