Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 93

Ka Albarkaci Taronmu

Ka Albarkaci Taronmu

(Ibraniyawa 10:​24, 25)

  1. 1. Ka albarkaci taronmu,

    Muna roƙo, Ya Allah.

    Mun gode domin taronmu

    Da ruhunka mai tsarki.

  2. 2. Ya Allah ka taimake mu

    Domin mu san Kalmarka.

    Muna so mu riƙa himma

    A yin wa’azin Mulki.

  3. 3. Ya Uba, muna roƙon ka

    Ka sa mu yi haɗin kai.

    Ayyukanmu, furucinmu,

    Su ɗaukaka ikonka.

(Ka kuma duba Zab. 22:22; 34:3; Isha. 50:⁠4.)