Koma ka ga abin da ke ciki

Yadda Aka Kāre Dabbobin da ke Chelmsford

Yadda Aka Kāre Dabbobin da ke Chelmsford

Shaidun Jehobah da ke Britaniya sun soma gina sabon ofishi kusa da birnin Chelmsford a yankin Essex. Akwai dabobbi dabam-dabam a wurin da suke ginin kuma gwamnatin Britaniya ta kafa doka don kāre dabobbin. Mene ne Shaidun Jehobah suka yi sa’ad da suke yin ginin don su bi wannan dokar da ta bukaci a kāre wadannan dabobbi?

Ana yi wa dabobbi hanya

Shaidun sun yi amfani da katakai da ke wurin da ake ginin don su kera gidajen da berayen jeji za su iya zama a ciki don kada su shiga wurin da ake aikin ba. Ban da haka ma, sun yi wa berayen hanyar da za su rika bi don su je kan bishiyoyin da kuma itatuwa. Kari ga haka, Shaidun suna bin wani tsarin gyara itatuwan musamman don berayen. A kowane shekara a lokacin da berayen suke hutawa Shaidun suna canja musu gida. Yin hakan yana taimaka wa don kada a rika damin berayen amma a tabbatar cewa an kāre gidansu kuma suna samun abinci yadda ya kamata a wurin.

Suna kera gidajen berayen jeji

Shaidun suna kāre majizai da kuma wasu irin kadangaru. Masanan mahalli suna kwasan wadannan dabobbi masu rarrafe daga karkashin rufi da aka ajiye su na dan lokaci kafin a kai su gidajen da aka gina musu da yake da nesa daga wurin aikin. A gidajen da aka gina don wadannan dabobbin masu rarrafe akwai sashen da za su rika hutawa da kuma bango. Shaidun suna duba wurin kowane lokaci don su tabbatar da cewa wadannan dabobbi masu rarrafe ba su dawo wurin aikin ba don za a iya yi musu rauni.

Beran jeji

Don kada a hana jemagu neman abinci daddare, an saka wani irin wuta a wurin aikin da zai rage yawan haske. Sai lokacin da motoci suke wucewa ne wannan wutar take yin haske, don jemagu din su kasance a cikin duhu. Saboda jemagu suna neman abinci da daddare a bishiyoyin da ke wurin da ake yin aikin, ba za a yanke yawancin bishiyoyin ba, kuma za a sake dasa wasu har zuwa rabin kilomita. Da yake ya zama dole a yayyanke wasu bishiyoyin da ke wurin da ake yin aikin, ma’aikatan sun gina gidajen da jemagun za su rika zama da yake sun yi rashin gidansu.

Saka gidajen jemagu

Ban da haka ma, Shaidun suna kāre wasu bishiyoyi da ake kiran su veteran kuma suna yin hakan ne ta wajen hana motocin aiki wucewa ta kan jijiyoyin bishiyoyin. Kuma wadannan bishiyoyin jemagu da tsuntsaye suna son zama a kansu. Ta yin wadannan abubuwan Shaidun sun kudiri aniyar ci gaba da kāre dabobbin da ke birnin Chelmsford.