Koma ka ga abin da ke ciki

Rumbun Hotunan Wallkill na (Nuwamba 2014 Zuwa Nuwamba 2015)

Rumbun Hotunan Wallkill na (Nuwamba 2014 Zuwa Nuwamba 2015)

A kwana kwanan nan, Shaidun Jehobah sun fadada da kuma kyautata gine-ginensu da ke garin Wallkill a jihar New York. A wannan rumbun hotuna za ka ga yadda aka yi wannan aikin daga watan Nuwamba 2014 zuwa Nuwamba 2015.

Hoton gine-ginen Wallkill da aka dauka daga sama a ranar 15 ga Oktoba, 2015.

  1. Wurin da Ake Buga Littattafai

  2. Ofisoshin Hidima na 1

  3. Gidan zama na E

  4. Gidan cin abinci

  5. Sashen wanki da guga

  6. Ofisoshin Hidima na 2

  7. Gidan zama na D

4 ga Disamba, 2014​—Ofisoshin Hidima na 2

Ana tsara yadda hanyar shiga sabon ofisoshin hidima za ta kasance. Ana gyara hanyar da mutane za su rika bi a hannu hagu don kada santsi ya kwashe su a lokacin sanyi. Akwai Ofishin hidima da Ofishin Kwamitin da ke kula da kasar da kuma Sashen Hidima a wannan ginin.

5 ga Disamba, 2014​—Gidan Zama na D

Wani da ke aiki a Sashen Tsara Dakuna yana amfani da wani inji da ke gyara daben ginin. Kuma akwai wani abu da ke rage kura a jikin injin din.

9 ga Janairu 2015​—Gidan Zama na E

Idan ka shigo za ka ga wurin da baki suke bi da kuma masu hidima fiye da 200 a Bethel da suke Gidan Zama na E. A wannan gyaran da aka yi, an saka wundo da zai sa a rage yawan amfani da wutar lantarki. Ban da haka ma, an saka wani abu da zai nuna idan gobara tana so ta tashi.

9 ga Fabrairu 2015​—Wurin da Ake Buga Littattafai

Wani mai gyaran wuta yana saka wayoyin tarho a sabon gini inda za a rika horar da mutane game da fasaha. An tsara wannan ginin don a koyar da mutanen da suke aikin famfo da wutar lantarki da kuma aikin tsaro.

17 ga Fabrairu 2015​—Wurin da Ake Buga Littattafai

Wata mai gyaran wuta tana saka wani irin kwan da ke rage yawan amfani da wuta a Sashen Fasaha.

2 ga Maris, 2015​—Ofisoshin Hidima na 1

Wata mai aikin wuta tana gwada wuraren da za a saka wuta. An gyara wurin nan don ya zama ofisoshin wadanda suka kauro daga Brooklyn.

3 ga Maris, 2015​—Gidan Zama na D

Wani mai aikin famfo yana gyara abubuwa kamar bututun da za su taimaka wajen ba da ruwan zafi.

31 ga Maris , 2015​—Gidan Zama na D

Wasu masu aiki a Sashen Tsara Gine-Gine sun hau lif suna saka abin da zai sa wundon ya zauna da kyau. Irin wadannan wundodi guda 298 da muke da su a wannan ginin suna taimaka wa wajen rage yawan kudin da ake kashewa a lokacin zafi da kuma lokacin sanyin.

17 ga Afrilu , 2015​—Ofisoshin Hidima na 1

Masu gini suna amfani da duwatsu don su gyara irin bangon da ake da shi tun daga shekara ta 1970 da wani abu a wurin da ake faka motoci tsakanin Ofisoshin Hidima da Gidan Zama na E.

17 ga Afrilu , 2015​—Ofisoshin Hidima na 1

Wani yana goge bango kafin a yi fenti. A wannan ginin ana da ofisoshin Lissafin kudi da sashen Kwamfuta da kuma sashen Saye-saye.

8 ga Yuni 2015​—Gidan Zama na D

Wani mai gyaran wuta yana jan waya zuwa rufin gidan. Wannan wayar za ta taimaka sa’ad da ake tsawa don kada ta yi barna a ginin.

8 ga Yuni 2015​—Gidan Zama na D

A lokacin da ake fadada ginin Wallkill, an mai da hankali sosai don kada a bata mahallin da ke wurin har da itatuwan da muke gani a wannan hoton. Wannan tankin ruwa da ke hagu yana iya rike ruwa lita 150,000. Kuma wurin ne ainihi ake samun ruwa a Wallkill da kuma ruwan da za a iya kashe gobara da shi.

25 ga Yuni 2015​—Ofisoshin Hidima na 1

Wani kafinta yana saka wasu bulo na katako 1,800 don ya zama bangon babban dakin taro. Wadannan bulon dabam-dabam ne kuma yana taimaka wa wajen hana jin kara a dakin.

9 ga Yuli, 2015​—Ofisoshin Hidima na 2

Dan’uwa Charles Reed ya soma hidima a Bethel tun shekara ta 1958. Ya taimaka wajen zana da kuma saka wasu abubuwa da suke taimaka wajen buga littattafai a lokacin da Bethel da ke Brooklyn take buga wa Amirka da wasu kasashe littattafai. A lokacin da ake aikin fadada Wallkill, Dan’uwa Reed ya yi aiki da wadanda suke bincika kyaun ginin.

17 ga Agusta, 2015—Ofisoshin Hidima na 1

’Yan’uwa suna saukar da kujerun da za a yi amfani da su a babban dakin taro. Wannan dakin taron zai dauki mutane 812.

21 ga Satumba , 2015​—Ofisoshin Hidima na 1

Gyaran wannan dakin taron ya kunshi saka su telibijin da wasu irin silin.

12 ga Oktoba , 2015​—Gidan Zama na D

Ana gyara wurin da nas nas za su rika aiki a asibiti. Ana fadada wuraren da za a rika jinya da kuma gidajen wanka.

15 ga Oktoba , 2015​—Wurin aiki a Wallkill

Hoton ginin Wallkill ke nan da masu hidima a Bethel guda 2,000 suke zama. An fadada wurin nan da ke da fadin mita 102,000 kuma akwai sabbin gine-gine a wurin ko kuma wuraren da aka gyara. An kammala wannan ginin a ranar 30 ga Nuwamba, 2015.