Koma ka ga abin da ke ciki

Me Ya Sa Shaidun Jehobah Ba Sa Bikin Ranar Haifuwa?

Me Ya Sa Shaidun Jehobah Ba Sa Bikin Ranar Haifuwa?

 Mu Shaidun Jehobah ba ma yin bikin ranar haifuwa don mu ga cewa irin wadannan bukukuwan suna bata wa Allah rai. Ko da yake Littafi Mai Tsarki bai gaya mana kai tsaye cewa kar mu yi bikin ranar haifuwa ba, akwai abubuwa da ya gaya mana da ke nuna yadda Allah yake ji game da bikin nan. Bari mu bincika hudu daga cikinsu.

  1.   Wadanda ba sa bauta wa Allah ne suka kirkiro bikin ranar haihuwa. Wani littafi da ya tattauna wannan batun ya ce mutanen da suka soma yin bikin ranar haifuwa sun soma yin hakan ne domin sun gaskata cewa aljannu sukan zo su cutar da mutum idan ranar haifuwarsa ta zagayo. Sun kuma gaskata cewa idan abokai sun taru kuma sun yi wa mutumin fatan alheri, hakan zai kāre shi daga hannun aljannu. Wani littafin kuma da ake kira The Lore of Birthdays ya ce: “A dā, masu yin duba da taurari sukan yi amfani da ranar haifuwar mutum ne wajen yin duba don su san abin da zai same shi a rayuwa.” Littafin ya kara da cewa, mutane sun yi imani cewa kandir da ake kunna wa a ranar haifuwar mutum za su iya sa ya sami duk abin da yake so a rayuwa.

     Amma Littafi Mai Tsarki ya haramta yin duba da sihiri da maitanci da “sauran irin abubuwa kamar haka.” (Maimaitawar Shari’a 18:14; Galatiyawa 5:19-21) Wani dalilin da ya sa Allah ya ce za a hallaka birnin Babila na dā shi ne don suna yin binciken taurari, wato suna amfani da taurari wajen yin duba. (Ishaya 47:11-15) Ba kowane biki ne Shaidun Jehobah suke kin yi don inda ya fito ba. Amma idan Littafi Mai Tsarki ya nuna sarai cewa tushensa bai dace ba, mukan bi abin da ya ce.

  2.   Kiristoci na farko ba su yi bikin ranar haifuwa ba. Littafin tarihi da ake kira The World Book Encyclopedia ya ce: “Kiristoci a dā sun gaskata cewa wadanda ba sa bauta wa Allah Madaukaki ne suke bikin ranar haifuwa.” Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa abin da ya kamata Kiristoci su yi shi ne su bi halin manzanni da wadanda Yesu da kansa ya koyar da su.—2 Tasalonikawa 3:6.

  3.   Abu daya ne kawai aka ce Kiristoci su rika tunawa da shi, wato mutuwar Yesu. (Luka 22:17-20) Hakan ya dace sosai domin Littafi Mai Tsarki ya ce, “ranar mutuwa . . . ta fi ranar haifuwa.” (Mai-Wa’azi 7:1) Yesu ya yi rayuwa mai kyau a duniya kafin ya mutu. Don haka, ya yi suna mai kyau shi ya sa ranar mutuwarsa ta fi ranar haifuwarsa muhimmanci.—Ibraniyawa 1:4.

  4.   Littafi Mai Tsarki bai taba cewa wani bawan Allah ya yi bikin ranar haifuwa ba. Da a ce ba a ambaci bikin ranar haifuwa a Littafi Mai Tsarki kwata-kwata ba, da sai mu ce mantuwa aka yi da wannan batun. Amma Littafi Mai Tsarki ya ba da labarin bikin ranar haihuwa biyu da wadanda ba sa bauta wa Allah suka yi. Kuma abubuwan da ya ce sun faru a wadannan bukukuwan sun nuna cewa wannan bikin, ba abin yi ba ne.—Farawa 40:20-22; Markus 6:21-29.

Shin yaran Shaidun Jehobah suna damuwa don ba a musu bikin ranar haifuwa?

 Shaidun Jehobah suna kaunar yaransu, sukan musu kyauta kuma su kira abokai su yi liyafa tare. Suna hakan a kullum, ba sa jira sai wani lokaci na musamman. Suna koyi da Allah wanda shi ma yake wa mutane alheri a kullum. (Matiyu 7:11) Ga abin da wasu yaran Shaidun Jehobah suka fada da ya nuna cewa ko da yake ba sa bikin ranar haifuwa, ba su rasa kome ba:

  •   Wata mai shekara 12 da ake kira Tammy ta ce: “Na fi jin dadi idan aka ba ni kyauta a lokacin da ban zata ba.”

  •   Wani yaro dan shekara 11 mai suna Gregory ya ce: “Ko da yake iyayena ba sa ba ni kyauta idan ranar haifuwata ta zagayo, sukan min kyauta a lokacin da ban yi tsammani ba. Abin da na fi so ke nan.”.

  •   Wani dan shekara 6 mai suna Eric ya ce: “Fati da ake yin minti goma, a rera waka kuma a ci dan kek, ai ba fati ba ne. Idan kana so ka ga yadda ake fati da gaske, ka zo gidanmu.”.