Koma ka ga abin da ke ciki

“Ina Yin Iya Kokarina”

“Ina Yin Iya Kokarina”

 Wata ’yar’uwa mai suna Irma a kasar Jamus ta kusan shekaru 90. Bayan ta yi hatsari masu tsanani so biyu da kuma tiyata, ba ta iya fita wa’azi gida-gida kamar yadda take yi a dā. A yanzu, Irma tana wa’azi ne ta wajen rubuta wasiku zuwa ga ’yan’uwanta da kuma abokanta. Wasikunta suna karfafa da kuma ta’anzantar da mutane, shi ya sa mutane sukan kira ta domin su san ranar da za ta tura musu wata wasikar. Ban da haka, sukan tura mata wasikun godiya da kuma nema ta kara tura musu wasiku. Irma ta ce: “Wadannan abubuwan suna sa ni farin ciki kuma suna taimaka mini in ci gaba da karfafa dangantakata da Allah.”

 Irma takan tura wasiku zuwa gidajen kula da tsofaffi, ta ce: “Wata tsohuwa da mijinta ya rasu ta kira ni ta waya ta ce wasikuna suna karfafata, kuma tana ajiye su a cikin Littafi Mai Tsarki don ta karanta, kuma takan yi hakan a kowace yamma. Wata mata kuma wadda mijinta bai dade da rasuwa ba, ta ce wasikuna suna taimaka mata fiye da wa’azin firist din cocinsu. Tana da tambayoyi da take son samun amsarsu ta ce in ziyarce ta in zan iya.”

 Wata mata abokiyar Irma da ba Mashaidiya ba ce ta kaura zuwa wani wuri mai nisa, amma ta ce Irma ta rika tura mata wasika. Irma ta ce : “Matar ta ajiye dukan wasikuna.” Ta kara cewa: “Bayan matar ta mutu, ’yarta ta kira ni ta waya kuma ta gaya mini cewa ta karanta dukan wasiku da na tura wa mahaifiyarta kuma ta ce in rika tura mata wasiku.”

 Irma tana jin dadin wa’azin sosai. Ta ce: “Ina rokon Jehobah ya ci gaba da ba ni karfin Bauta masa. Ko da yake ba na iya zuwa wa’azi gida-gida amma ina yin iya kokarina.”