Koma ka ga abin da ke ciki

Yadda Muke Amfani da Rumbun Bayanai

Yadda Muke Amfani da Rumbun Bayanai

ABIN DA MUKE YI DA BAYANANKU

A wannan dandalin, za ka iya yin amfani da shafuffuka da dama ba tare da ka yi rajista ko kuma ka ba mu wani bayani game da kanka ba. Amma akwai wasu sashen dandalin nan da za a bukace ka ka yi rajista ko kuma ka ba da bayani game da kanka kafin a ba ka izinin amfani da su. Kamar idan kana son ka aika bukata da kanka ko ta wurin ikilisiyar Shaidun Jehobah. Za mu bincika bayaninka da amincewarka. In ka ce ba ka son mu bincika bayaninka, daga baya kuma ka ce mu yi hakan, za mu iya ci gaba da bincika bayaninka ne muddin ka bi tsarin da doka ta tanadar.

Kafin ka aika mana bayaninka, za mu gaya maka abubuwan da muke so mu yi amfani da su. Abubuwan nan sun ƙunshi:

Shafinka Na JW. Adireshinka na imel da ka tanadar sa’ad da kake shiga dandalin nan ne za a yi amfani da shi don a ba ka bayanai game da shafinka na JW. Alal misali, idan ka manta da sunan da ka yi amfani da shi ko kuma kalmar sirri na shiga dandalin, za mu iya taimaka maka ta wajen aika maka sako game da hakan a imel ɗinka.

In Kana da Bukata. Kana iya yin amfani da dandalin nan don ka aika bukatarka ko kuma ka sa dattawa a ikilisiyarku su aika maka. Za mu yi amfani da bayanin da ka tanadar don mu yi aiki a kan bukatar da ka tura da kuma wasu abubuwa game da hakan. A wasu lokuta, in ya zama dole, muna ba ’yan’uwanmu ko kuma wasu mutanen da ƙungiyar Shaidun Jehobah take amfani da su da ke wasu ƙasashe bayaninka don su yi aiki a kan bukatar da ka tura.

Gudummawa. Idan kana so ka ba da gudummawa ta intane, za mu karbi sunanka da lambar wayarka da kuma adireshinka. Idan kana so ka yi amfani da katin ATM ne, ka san cewa wannan hanyar a tsare take kuma za a kāre sirrinka. Za mu bukaci wasu bayanai game da bankinka, kamar lambar da ke katin ATM ɗinka da kuma lambar bankinka, sai mu tura wa waɗanda za su yi aiki a kai. Muna mai da hankali sosai sa’ad da muke aiki a kan gudummawar da ka ba da kuma hanyar da muke bi daidai ne da wanda Payment Card Industry Data Security Standard (“PCI DSS”) ta tanadar. Akwai wani da yake ajiye rahotanni game da gudummawar da ka bayar har na wajen shekara 10. Rahoton ya haɗa da ranar da ka ba da gudummawar, da yawan kuɗin da ka bayar da kuma hanyar da ka yi amfani da shi. Hakan zai taimaka mana mu bi tsarin da banki suke bi kuma mu iya ba da amsa ga tambayoyin da kake da shi. Ba za mu kira ka ka tura maka sakon cewa muna bukatar karin gudummawa ba.

Neman Karin Bayani Ko Kuma Nazarin Littafi Mai Tsarki. A dandalinmu, kana iya neman karin bayani ko kuma ka ce a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kai. Za mu yi amfani da bayanin da ka bayar don mu taimaka maka saboda da wannan dalilin kawai. In ya zama dole, za mu ba wa ’yan’uwanmu ko kuma wasu mutanen da ƙungiyar Shaidun Jehobah take amfani da su da ke wasu ƙasashe bayaninka don a yi aiki a kan bukatarka da ka tura.

Wasu Abubuwa. Kana iya tura mana bayanin game da kai (kamar sunanka da adireshinka da kuma lambar wayarka) don wasu abubuwa ban da shiga shafin dandalin ko aika bukata ko kuma yin gudummawa. Za mu gaya maka dalilin da ya sa muke bukatar ka ba mu bayani game da kanka. Ba za mu taba yin amfani da bayaninka wajen gudanar da wasu abubuwan da ba mu gaya maka ba.

Za mu karbi bayaninka, mu ajiye su kuma mu yi amfani da su don abubuwan da muka gaya maka kawai. Muna ajiye bayaninka ne idan da bukatar yin hakan. Idan ka ki ka ba mu wasu bayananka, ba za ka iya shiga wasu shafuffuka a dandalin ba kuma ba za mu iya yin aiki a kan bukatarka ba.

Mutanen da suke da ’yancin duban bayanan da ka aika ne kawai za su iya ganin bayaninka. Ba za mu ba wa kowa bayaninka ba sai dai (1) in ya wajaba mu yi hakan don a yi aiki a kan bukatarka kuma mun gaya maka hakan; (2) in mu ga cewa yin hakan bai zai taka doka ba; (3) in hukumar da ke aiki a kan bukatarka ta bukaci hakan; ko kuma (4) in ana so a yi amfani da shi don a kāre wasu matsaloli kamar damfara. Idan ka soma amfani da dandalin nan, ka amince cewa mu ba wa hukuma bayaninka. Ba za mu sayar ko ka ba aron bayaninka da ka bayar ba.

AIKA BAYANINKU TURAI

Wannan kungiyar tana gudanar da harkokinta a wurare da yawa a fadin duniya. Wasu ma’aikatan da ke kula da dandalin nan suna Amirka. Don haka, muna iya aika bayaninka zuwa wasu kasashen da watakila dokokinsu da kuma kariyarsu ba daya ba ne da na kasarka. Amma muna iya kokarinmu don mu kāre bayananka sa’ad da muke tura su wasu kasashe. Wajibi ne mutanen da muke amfani da su don fadada ayyukan Shaidun Jehobah su bi tsarin kariyar da muka tanadar da kuma dokar da muka kafa a kan bayananku.

Ta wajen yin amfani da dandalin nan da kuma tattaunawa da mu ta intane, ka amince da wannan tanadi na aika bayaninka zuwa wasu kasashe.

’YANCIN DA KAKE DA SHI

Idan muka karbi bayaninka, muna tabbatawa cewa bayanin daidai don dalilin da ya sa aka bukace shi. A duk kasar da kake kana ’yancin a kan bayananka da ka ba mu:

  • Kana da ’yancin ka ce mu ba ka rahoto a kan yadda ake amfani da bayaninka;

  • Kana da ’yancin gaya mana mu ba ka damar gyara ko canja bayaninka ko kuma ka rufe bayaninka idan ba daidai ba ne;

  • Kana iya gaya mana cewa ba ka son yadda ake amfani da bayaninka kuma mun daina yin hakan idan kana da kwakkwarar dalilin yin hakan.

Idan kasar da kake tana da nata doka aka tsare sirrin bayanin mutum, kuma kana so ka gyara ko canja bayaninka, za ka ga bayanin a shafin Data Protection Contacts.

Bayan ka ba da isashen bayaninka game da kanka kuma ka aika mana bukatarka, wanda zai yi aiki a kan bukatar zai auna sosai ya ga ko bukatar zai amfani kungiyar. Zai yi bincike ya ga ko bukatarka za ta iya sa ’yancin da kungiyar take da shi na yin ayyukan ibada cikin hadari. Kari ga haka, za mu gaya wa wata kungiyar game da canji da aka yi game da bukatarka.

Don Allah ka san cewa ba za ka iya goge bayananka ba idan hukuma ne suke aiki a kai ko kuma idan aka ajiye bayanan don wasu abubuwa da ya shafi shari’a. Alal misali, kungiyar tana son ta ajiye bayani game da wani Mashaidin Jehobah har abada. Idan aka goge wannan bayanin, hakan ya keta dokar da kungiyar ta kafa. Don haka, ba za mu goge bayanin ba sai da in hukumar ta bukata ce mu mu yi hakan. Ban da haka, kana iya gaya wa hukumomin kasarku idan ka ga kuskure a kan yadda ake amfani da bayaninka da ka tanadar a wannan dandalin.