Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 52

Alkawarinmu ga Jehobah

Alkawarinmu ga Jehobah

(Ibraniyawa 10:​7, 9)

  1. 1. Allah Jehobah ne ya yi

    Sammai da duniya.

    Shi ne ya halicci kome,

    Duk ayyukansa ne.

    Ya ba da rai ga ’yan Adam

    Da kuma dabbobi.

    Shi ne Allahn da ya cancanci

    Yabo da kuma bauta.

  2. 2. Ɗan Allah ya yi baftisma

    Domin amincinsa.

    Ya ce wa Mahaliccinsa:

    ‘Na zo yin nufinka.’

    Sa’ad da ya yi baftisma

    Ya zama shafaffe.

    Ya yi addu’a ga Allahnsa:

    ‘Uba a yi nufinka.’

  3. 3. Mun zo gabanka, Jehobah,

    Domin mu bauta ma.

    Mun ba ka duk rayuwarmu

    Don mu yi nufinka.

    Ɗanka ya zo duniyar nan

    Domin ya fanshe mu.

    Ko mun mutu ko muna raye,

    Mu naka ne koyaushe.

(Ka kuma duba Mat. 16:24; Mar. 8:34; Luk. 9:23.)