Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ba Zan Ji Tsoro Ba

Ba Zan Ji Tsoro Ba

Ka Saukar:

  1. 1. 1. Na shirya zan fita da sassafen nan,

    Sai na tuna an hana mu waꞌazi.

    Ni ba zan daina ba, ya Allah ga ni,

    Taimake ni don kai nake bi.

    (AMSHI)

    Na san ka fi karfin su ja da kai, Ubangijinmu.

    Ba zan ji tsoro ba sam, me za su yi min?

    Ba zan ji tsoro ba sam, me za su yi min?

  2. 2. Da na fita sai na ga wani mutum,

    Mutumin yana cikin damuwa.

    Ya Jehobah sai ka sake hada mu,

    Na san zai ji dadin jin maganarka.

    (AMSHI)

    Na san ka fi karfin su ja da kai, Ubangijinmu.

    Ba zan ji tsoro ba sam, me za su yi min?

    Ba zan ji tsoro ba sam, me za su yi min?

  3. 3. Na gaji da rike maganarka

    A zuciyata, Ya Allahna.

    Zan yi waꞌazin babu tsoro.

    Zan yi waꞌazin nan har zuwa karshe.

    Na san ꞌyanꞌuwana kuna hakan

    A duk duniya, kar mu daina.

    Allah na sama zai taimake mu.

    A nan gaba zai ba mu aljanna.

  4. 4. Dare ya yi bari in yi barci,

    Amma zan gode ma Allah tukun.

    Na tabbata ko da me zai faru,

    Ubangiji zai taimaka mini.

    (AMSHI)

    Na san ka fi karfin su ja da kai, Ubangijinmu.

    Ba zan ji tsoro ba sam, me za su yi min?

    Ba zan ji tsoro ba sam, me za su yi min?